Mrs Mabel Ijeoma Duaka ma’aikaciyar jinya ce a ƙaramar hukumar Mafa, ta fara aiki ne a shekarar 2004.
An haife ne ta ga iyalan marigayi Mr Obed Duaka da Mrs Catherine Duaka a shekarar 1964, ita ce ta farko a cikin su 8 da Allah azurta iyalan da shi, sha’awarta na warkar da mara lafiya ya sanya ta canza aiki daga malamar makaranta a Wulari II Primary School da ke Maiduguri (inda ta fara aiki bayan ta kammala karatu) inda ta nemi gurbi a Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Maiduguri (UMTH) inda ta yi karatun jinya daga shekarar 1985 zuwa 1990.
Bayan kamala karatu Mrs Duaka ta yi aiki na wucin gadi a matsayin Nas kafin ta samu aiki na dindindin a Ƙaramar Asibitin garin Mafa a shekarar 2004.
- Sheriff Oboreɓwori: Gwamnan Da Ya Ginu Kan Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Ci Gaban Al’umma
- Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025, Injiniya Abdullahi Sule
A kokarinta na kara inganta aikinta na jinya, Mrs Duaka ta wuce Jami’ar Maiduguri, inda ta samu digiri a aikin jinya B. Sc Nursing ta hanyar tallafin karatu da gwamnatin Jihar Borno ta bayar. A kokarinta na yi wa waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa waɗanda suka rasa matsugunansu a Mafa zuwa sansanin ‘yan gudun hijira da ke wajen garin da ke kusa da Maiduguri, Misis Duaka ta yi aiki tuƙuru a sansanin, tare da kula da lafiyar ‘yan gudun hijirar har zuwa lokacin da zaman lafiya ya dawo Mafa kuma aka sake tsugunar da su a shekarar 2016.
Tun daga wannan lokacin, ta ci gaba da zama a Mafa tana yin abin da ta fi so – tana ba da taimakon kiwon lafiya na musamman ga marasa lafiya, ko a cibiyar kula da lafiya na farko, a cikin gidaje ko kuma a sansanonin da aka kafa don ‘yan gudun hijirar da ‘yan ta’adda suka lalata gidajensu.
Ana haka ne Gwamna Babagana Umara Zulum ya kai ziyara ƙaramar hukumar, inda ya gana da Misis Duaka a cibiyar lafiya da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da sauran ma’aikatan duk sun tashi. Wannan aiki na sadaukarwa, juriya da biyayya ga aikinta, ya sa Gwamna Zulum ya fahimci cewa ta himmatu wajen kula da lafiyar mutanen Mafa, mahaifar sa. Gwamnan dai a wasu ziyarce-ziyarcen da ya kai har sau biyu, ya ware ta, ya kuma yaba wa sadaukarwar da ta yi, tare da yaba mata kan yadda ta tsaya tare da jama’arsa duk kuwa it aba ‘yar asalin yankin ba ne.
Kyautar kwazo da rikon amana da ta samu ya zo ne a lokacin da Gwamna Zulum, wanda ya yi fice wajen bayar da lada ga ƙwazo, ya haɗa da Mrs Duaka a cikin malamai 72 da ma’aikatan lafiya da suka samu gidajen kwana a wani biki da aka ƙaddamar a garin Mafa.
Yayin gabatar da makullan, gwamnan ya kuma sanar da ɗaukar aiki kai tsaye ga ɗanta Anthony, wanda ya kammala karatun Harkokin Banki, a Jami’ar Kashim Ibrahim ta jihar.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa Mrs Duaka ta shafe sama da shekaru ashirin tana aiki a cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Mafa, kuma ba ta bar garin ba, ko da lokacin da ake fama da rikicin Boko Haram. Da yake ƙarin godiya, gwamnan ya bayyana cewa ta yi aiki a Mafa sama da shekaru 24 ba tare da barin garin ba na tsawon wata guda. A lokacin rikicin, lokacin da mafi yawan mutane suka gudu, ta zauna tana kula da al’ummar garin ciki har da mahaifiyarsa.
Mrs Duaka na da aure da ‘ya’ya 4.












