Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, ya ce, har sai an cika sashe na 7 na kundin tsarin mulkin Nijeriya kafin gwamnoni su daina sama da fadi da kudaden kananan hukumomi.
Gwamnan, ya bayyana hakan ne yayin da ya ke rattaba hannu a kan kasafin kudin jihar na 2023 naira biliyan 166.985, 110. 21 a gidan gwamnatin da ke Birnin Kebbi.
- Shugaba Xi Ya Aikewa Shugaba Cyril Ramaphosa Sakon Taya Shi Murnar Sake Zaben Sa A Matsayin Shugaban Jam’iyyar ANC
- Ba Tsige Ni Aka Yi Ba, Ni Na Yi Murabus Da Kaina – Baba ImpossibleÂ
Ya ce, ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi na tafiya a dukkan majalisun jihohi, dole ne a amince da majalisar dokokin kasar nan na yi wa sashe na 7 na kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.
Kazalika, ya kara da cewa gwamnatinsa ba ta hana cin gashin kan kananan hukumomi ba kamar yadda ake yadawa.
“Kebbi ba son a bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai da na ma’aikatar shari’a.
“A makon da ya gabata, an gudanar da taron hadin gwiwa na dukkan gwamnoni da shugabannin majalisun jihohi, inda na gabatar da batutuwa kan wannan batu da kuma batun tsaro.
“Na ce ya kamata majalisar dokokin kasa ta bai wa majalisun jihohi ikon tunkarar kalubalen tsaro a jihohinsu.
“Kuma ya kamata ya kasance su na da ikon nada jami’an shari’a da kuma tsige su. Na ce, Idan majalisar dokokin jihar na da ikon tsige gwamna to ya kamata ta sami ikon sarrafa bangaren shari’a,” in ji Gwamna Bagudu.
Ya ce kasafin kudin 2023 da ya sanya wa hannu, ya zama doka gwamnatoci biyu ne za su aiwatar da shi domin za ya bar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
“Saboda yadda kasafin kudinmu na bankin duniya da sauran hukumomin kasa da kasa suka sanya Jihar Kebbi a matsayin daya daga cikin jihohin kasar nan da suka yi amfani da kasafin kudinsu yadda ya kamata.
“Kuma hakan ya sa jihar Kebbi ta samu lambar yabo guda biyar a cikin watannin da suka gabata, in ji shi”.