A yau Asabar 31 ga wata ne, babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikewa shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, sakon taya shi murnar sake zaben sa a matsayin shugaban jam’iyyar ANC mai mulkin kasar.
Cikin sakon na sa, shugaba Xi ya ce JKS da jam’iyyar ANC, sun kulla kyakkyawan kawance na gargajiya, sun kuma cimma nasarori a fannin musaya da hadin gwiwa, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa a fannin zurfafa ci gaban cikakkiyar hadin gwiwarsu bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni.
Shugaban na Sin ya ce a shirye yake, ya yi aiki tare da shugaba Ramaphosa, wajen daga matsayin alakar jam’iyyun 2, da kasashen zuwa sabon matsayi, da gina al’umma mai makomar bai daya ga kasashen Afrika da ma daukacin bil Adama a sabon zamani. (Saminu Alhassan)