Kwamitin majalisar wakilai kan albartun kasa, ya ce Nijeriya tana tafka asarar naira biliyan 9 a kowace shekara sakamakon aikace-aikacen masu hakar ma’adinai ta haramtattun hanyoyi a Nijeriya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin Nijeriya ta ce, ta cafke wadanda take zargi da hannu a hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba su 387 a cikin watanni bakwai da suka gabata.
- Ramin Haƙar Ma’adanai Ya Rufta Da Mutum 3 A Jihar Neja
- Miyar Agushi Mai Dadi Irin Ta Yammacin Nijeriya
Shugaban kwamitin majalisar, Jonathan Gaza Gbefwi, shi ne ya shaida hakan a yayin taron jin bahasin jama’a da kwamitin ya shirya kan binciken lamuran da suka shafi hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da na albartun kasa. Ya ce, wannan mummunar ayyukan satar ma’adinai ya janyo takaituwar jin gajiyar albartun da jama’an kasa ba su yi yadda ya dace.
Ya koka kan cewa zallar kaso uku kawai cikin kamfanonin da ke hakar ma’adinai ne suka biya na kudin lasisi hakar ma’adinai a kasar nan.
A cewarsa, daga cikin illar da hako ma’adinai ta barauniyar hanya ke janyowa har da janyo matsalolin tsaro da kuma arangama kan wake ko su waye masu ikon jan ragamar wuraren hako ma’adinai da albartun da ke ciki.
Ya ce, irin wannan rigimar na fantsama har ya shafi siyasa da zamantakewar jama’an da ke yankunan da abun ya shafa, wanda hakan ba daidai ba ne sam.
Sannan ya kara da cewa taron jin bahasin an shirya ne da zimmar shawo kan matsalolin da suke tattare da aikace-aikacen hako ma’adinai da kuma inganta hanyoyin samar da lasisi domin kyautata samar wa kasar nan da kudaden shiga da kuma cin gajiyar ma’adinan da suke jibge a kasar ba tare da wasu matsaloli ba.
“Nijeriya tana rasa naira biliyan 9 a kowace shekara kan ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba. Don haka, jagorancin majalisar wakilai ta 10 ya ga dacewar ya ji bahasin jama’a domin kawo gyara da mafita cikin wannan lamarin ta yadda za a samu gaskiya da adalci kan kudaden da suke shigowa domin inganta tattalin arzikin kasa.
“Ta’asar masu hako ma’adinai ba bisa ka’ida na gurgunta ci gaban da ake samu a bangaren ma’adinai, kuma yana janyo lalata muhalli da gurbacewarsa wanda ke janyo asarar kudaden shiga masu tulin yawa da ya dace jama’an da ke yankunan da abun ya shafa da ma kasa su mora.”
A fadin Jonathan, akwai bukatar a gaggauta daukan matakan da suak dace wajen dakile aniyar masu satar ma’adinai domin kyautata kudin shiga, kare jama’a da kuma tabbatar da duk masu hakar ma’adinai na bin dokokin kasa.
Shi kuma, shugaban sojojin Nijeriya, Janaral Christopher Musa, ya ce masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba suna samun goyon baya daga wasu fitattun mutane da suke ba su kariya.
Da yake bude taron jin bahasin jama’an, kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, wanda ya samu wakilcin Farfesa Julius Ihonbbere, ya lura kan cewa satar ma’adinai na ruguza tattalin arzikin kasar nan, lamarin da a cewarsa yake kara jefa jama’a cikin fatara da talauci, musamman manoman da suka dogara da noma amma aka lalata musu muhallin da suke zama da sunan hakar ma’adinai.