Erling Haaland ya jefa kwallaye uku yayin da Manchester City ta ci gaba da jan zarenta a Premier inda ta doke Fulham da ci 5-1 a ranar Asabar.
Zakarun na Ingila sun kasance ba tare da koci Pep Guardiola ba yayinda yake cigaba da murmurewa daga tiyatar da aka yi masa a baya a yankinsa na Catalonia.
Julian Alvarez ya zura kwallo a ragar Haaland a minti na 31 kafin Haaland ya jefa tasa bayan an dawo hutun rabin lokaci.
Abinda yasa ya zama dan wasa da ya ci kwallaye 40 a gasar Premier, a cikin wasanni 39 kawai.
Gab da tashi wasan Haaland ya zura kwallonsa ta uku a wasan kuma ta 6 jimilla a wannan kakar wasa ta bana.