Gwarzon dan kwallon kafa da ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Erling Braudt Haaland, ya kafa tarihi a gasar Firimiya inda ya zama dan wasa na farko a tarihin gasar da ya lashe kyautar gwarzon shekara da kuma gwarzon matashi.
Haaland wanda ya koma Manchester City daga Borussia Dortmund kan kudi Yuro miliyan 65, ya zura kwallaye 52 a bana; 36 a Firimiya, hakan ya sa ya karya tarihin da tsohon kyaftin din Newscastle United Alan Shearer ya kafa.
Manchester City na kan hanyarta na lashe kofuna uku a kaka daya bayan ta lashe gasar Firimiya, inda za ta Kara da abokiyar hamayyarta Manchester United a wasan karshe na kofin kalubale na FA kafin ta buga da kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan a wasan karshe na kofin zakarun turai ranar 10 ga watan Yuni.
Za a buga wasan a filin wasa na Ataturk da ke Santanbul ta kasar Turkiyya, idan ta iya lashe sauran kofunan za ta zama kungiyar da ke Ingila ta biyu da za ta lashe kofuna uku a kaka daya bayan Manchester United.