Dan kwallon kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Erling Haaland ya samu rauni kafarsa yayin da buga wani wasan sada zumunta da kasarsa ta Norway ta buga.
Mai horas da ‘yan wasan kwallon kafa ta Manchester City da magoya bayan ba su ji dadin wannan labarin jin raunin dan wasansu Haaland ba, Haaland wanda ya jefa kwallaye 17 a wasannin 18 da ya buga a bana.
- Manchester United Zata Karbi Bakuncin Brentford A Filin Wasa Na Old Trafford
- Tsohon Dan Wasan Manchester United, Charlton Ya Mutu
Likitan tawagar kasar Norway Ola Sand ya bayyana cewar Haaland ya ji rauni a daidai inda ya yi fama jinya a kwanakin baya.
Manchester City dai zata kara da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a kwanaki 9 masu zuwa a gasar Firimiya Lig ta kasar Ingila.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp