Shugaban kamfani dake lura da ci gaban yankunan masana’antu na kasar Habasha ko IPDC mista Fisseha Yitagesu, ya jinjinawa masu zuba jari na kasar Sin, bisa muhimmiyar gudummawar su ga bunkasar tattalin arzikin kasar Habasha, da yadda suke taimakawa sashen samar da guraben ayyukan yi na kasar, karkashin ayyukan dake gudana a yankunan masana’antu, da yankin gudanar da cinikayya maras shinge na farko a kasar.
Cikin wata sanarwa da mista Yitagesu ya fitar a ranar Laraba, yayin ganawarsa da wasu Sinawa masu burin zuba jari a yankunan masana’antu na kasar ta Habasha, ya ce Sinawa masu zuba jari ne kan gaba wajen gudanar da hada hada a dukkanin yankunan raya masana’antu 13 dake kasar, da ma sabon yankin gudanar da cinikayya maras shinge na kasar da aka bude a Dire Dawa, wanda kamfanin IPDCn ke kula da shi.
Jami’in ya kara da cewa, sama da kamfanonin Sinawa 40 ne ke gudanar da ayyuka a yankunan na masana’antu, inda suka samar da guraben ayyukan yi sama da 25,000 musamman ga matasan kasar ta Habasha. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp