Alkaluman hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna cewa a watan Afirilun bana, hada-hadar cinikayyar shige da ficen hajoji ta amfani da kudin kasar yuan ta karu da kaso 5.6 bisa dari.
Alkaluman da hukumar ta fitar a Juma’ar nan sun nuna cewa, adadin hajojin da kasar Sin ta fitar ya karu da kaso 9.3 bisa dari a shekara zuwa yuan tiriliyan 2.27, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 314, yayin da adadin hajojin da kasar ta shigo da su daga waje ya karu da kaso 0.8 bisa dari a shekara zuwa kimanin yuan tiriliyan 1.57.
Cikin watanni 4 na farkon shekarar bana, jimillar hajojin da Sin ta shigo da su, da wadanda ta fitar ketare a hada-hadar kudin kasar yuan sun karu da kaso 2.4 bisa dari zuwa yuan tiriliyan 14.14.
Tsakanin wannan wa’adi, Sin ta fitar da hajojin da suka karu da kaso 7.5 bisa dari, wato na kimanin yuan tiriliyan 8.39, yayin da adadin hajojin da ta fitar suka ragu da kaso 4.2 bisa dari zuwa yuan tiriliyan 5.75. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp