Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) ta tabbatar da cewa jamianta 4 sun rasu yayin da wasu 7 suka ji raunuka a wani hadarin mota da ya rusa da su a Jihar Kano.
Mai magana da yawun hukumar, DCI Adedotun Aridegbe ya bayyana haka a shalkwatar hukumar a wani taron manema labarai da ya kira ranar Litinin.
Ya yi bayanin cewa, A jiya ne wasu maaikatanmu goma sha daya ke dawowa Abuja daga wani aiki a Kano, a cikin wata motar bas mai daukar kujeru goma sha takwas suka yi wani mumunar hatsari, a wani wuri yan kilomitoci kadan daga Kano. Sakamakon haka, maaikatanmu hudu sun rasa rayukansu. Wannan lokaci ne na jimami a Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya.
Abokan aikinmu guda bakwai da suka samu raunuka daban-daban a halin yanzu suna karbar magani a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Kano. Muna musu adduar samun lafiya cikin gaggawa.
- ‘Yansanda Sun Cafke Malamin Addini Da Sassan Mutum Danye A Oyo
- Nijeriya Da Saudiyya Sun Kulla Alakar Musayar Fasaha A Bangaren Mai
Hukumar ta bayyana cewa, ta sanar da iyalan jamian da abin ya shafa kafin ta kira taron manema labarai don bayyana wa duniya asalin abin da ya faru, inda yanzu haka ake shirin yi wa wadanda suka mutu janaiza ta bangirma.
Mukaddashiyar Kwanturola Janar ta Hukumar Kula da Shige da Fice, Caroline Wura-Ola Adepoju, ta yi matukar bakin ciki da wannan rashi, kuma da kanta ta mika ta’aziyya ga iyalan mamata tare da nanata cewa hukumar tana tare da iyalan magidantan da suka mutu cikin tallafawa a wannan lokaci na alhini. In ji shi.
Adedotun ya kuma ce, tuni Mukaddashiyar Kwanturola Janar ta ba da umarnin gudanar da bincike nan take don gano musabbabin hadarin. Kana ta sha alwashin daukar matakan da suka dace don hana faruwar hakan nan gaba.
Wannan lokaci ne na jimami a tsakanin daukacin iyalan Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya. Mukaddashiyar CGI ta umurci dukkan ofisoshi da rassan hukumar su sassauta tutocinsu na tsawon kwanaki bakwai masu zuwa. Za mu kuma yi zaman makoki na kwanaki uku don girmamawa da tunawa da abokan aikinmu da suka mutu. In mai magana da yawun hukumar.