Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa (CITAD), ta horas da yan mata ashirin da biyar da aka zakulo daga sassan Nijeriya kan yadda za su shiga a dama da su wajen fasahar sadarwar zamani da jagoranci.
Da take magana da yan jarida a yayin horon na kwanaki biyu da ya gudana a Bauchi makon jiya, jamiar kula da bangaren jinsi na CITAD, Zainab Aminu, ta ce, an zabo matan ne kuma an ba su horo na musamman a bangarorin shugabanci ta yadda za su shiga a dama da su a bangaren fasahar sadarwa tare da fuskantar kalubalen da mata ke fuskanta dangane da mu’amala da fasahar zamani.
- CITAD Ta Bai Wa ‘Yan Jarida 10 Tallafi Don Gudanar Da Bincike Game Da Cin Hanci
- Manyan Kalubalen Da Ke Durkusar Da Kiwon Kifi A Nijeriya
Ta ce, matan sun kuma samu horon yadda za su rungumi bangaren ICT domin shawo kan wariyar da ake yi wa mata a wannan fannin da kuma basu damar shiga a dama da su a bangaren fasahar sadarwa, hadi da tsare-tsaren da suka shafi kyautata harkokin jinsi.
Jamiar ta kara da cewa bangarorin da horon ya kuma maida hankali sun hada da tsare-tsaren fasahar sadarwa, matakan amfani da yanar gizo, hanyoyin da ake amfani da kafafen sadarwa ba tare da wani musgunawa ko cin zarafinsu ba, hadi da tsare-tsaren yadda za su samu damar kirkirar abubuwa tare da samar da damarmaki ga mata.
Zainab Aminu ta kara da cewa, lokaci ya yi da mata za su amfana da dukkanin damarmakin da ke cikin fasahar zamani ba tare da tsangwama ba.
Wannan horaswar ta jagoranci na da manufar wayar da kan mata kan yadda za su samu damar shiga a dama da su kan tsare-tsare da yadda za su shiga a yi da su a bangaren ICT da kuma dabarun yadda za su samu ilimi kan sauye-sauye, ta shaida.
Ita ma da take magana, daraktan cibiyar kere-kere ta Bloom, Hannah Kabrang, ta ce, horaswar zai taimakesu wajen kara samun damarmakin yadda za su fuskanci tsare-tsaren fasahar sadarwa da kuma yadda za su taimaki mata su shiga a dama da su wajen amfanuwa da zamani.
Ita ma Sadiya Lawan, daliba a jamiar Dutsin-Ma, da ta kasance mahalarciyar taron, ta ce, sun samu gogewar yadda za su fuskanci kowani irin kalubalen da ke fuskantar mata a kafafen sadarwar zamani da kuma fasahar zamani gaba daya.
Tana mai cewa an kuma basu horon ta yadda su ma za su koyar da wasu yadda za su fuskanci wadannan matsalolin da mata ke fuskanta musamman a kasar nan.