Hukumar kiyaye haddura ta jihar Ogun (TRACE) ta tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da jikkatar wani sanadiyar hadarin da ya rutsa da wasu motoci kirar Mazda Bas guda biyu da suka yi taho mu gamu a yankin Ayedere da ke babbar hanyar Lagos zuwa garin Abeokuta.
An rahoto cewa, direban dayar motar ne wacce ba ta dauke da lamba ne ya haddasa hadarin inda ya yi karo da Mazda bas mai dauke da lamba SEY 311 ZY.
Kakakin hukumar TRACE, Babatunde Akinbiyi wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ga manema labarai a garin Abeokuta ya ce, Direbobin motocin sun rasa rayukansu nan take inda kuma yaron motar, ya samu raunuka.
Yaron motar da ya samu raunuka an kaishi Asibiti mafi kusa kafin zuwan jami’an hukumar, daya daga cikin Direbobin da suka rasu, ‘yan uwanshi sun dauke shi domin yi masa jana’iza, na biyun kuma an kai gawarsa dakin ajiye gawarwaki da ke Babban Asibitin Ifo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp