Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya muku yadda ake Grailled Chicken wato gasasshiyar kaza.
Abubuwan da za ku tanada:
Kaza, Takaddar Nade Nama wato (Foil paper) Magi, Gishiri, Kori, kayan yaji da kayan kamshi, Albasa:
Yadda za ku hada:
Da farko za ku wanke kazar sosai, sannan ku zuba a kwando ku ajiye ta, ruwan jikinta ya tsame sosai, Sannan ku samu wata ruba ku zuba ta sai ku yanka Albasa akai sannan ku zuba Magi, Gishiri, da Kori da kayan yaji da kuma kayan Kamshi ku zuba su daidai yadda zai isa ya yi dadi sai ku gauraya ko’ina ajikin kazar ku shasshafa ya shisshiga jikin kazar, sannan ku kawo Foul paper sai ku wari daidai yadda za ku zuba kazar, sannan ku zuba kazar a ciki ku rufe shi ya rufu sosai ko ina ki kodindine sai ku saka shi a firiza ya yi kamar awa daya kafin nan ya kama jikinsa sai ku dakko shi ku saka shi a Oben wato abin kashi sai ku gasa shi yayi kamar awa daya da rabi zuwa biyu kuna yi kuna dubawa idan kasa ya gasu sai ku juya saman ma ya kasu.
A ci dadi lafiya.