Kwararru mahalarta taron karawa juna sani karo na uku, game da nazarin halin zaman lafiya da ci gaba da ake ciki a yankin kahon Afirka, sun ce jarin da kasar Sin ke zubawa a fannonin tattalin arziki, da shirye-shiryen raya zamantakewar al’umma, sun haifar da ci gaba, a kokarin da ake yi na zamanantar da yankin na kahon Afirka, musamman duba da yadda tashe-tashen hankula, da tasirin sauyin yanayi suke dakile ci gaban kasashensa.
Yayin taron na jiya Alhamis da ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya, jakadan musamman na kasar Sin dangane da harkokin da suka shafi yankin kahon Afirka a ma’aikatar harkokin wajen Sin Xue Bing, ya ce Sin ta jima tana goyon bayan manufofin raya cudanyar sassa daban daban, ta yadda za a samar da ci gaba na tsawon lokaci, da zaman lafiya da daidaito a yankin.
- An Kafa Fiye Da Kamfanonin Waje 24,000 A Sin Cikin Watanni 5 Na Farkon Bana
- Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya: Akwai Babban Aiki A Gaban Nijeriya
Xue ya kara da cewa, taron na karawa juna sani game da nazarin halin zaman lafiya, da ci gaban yankin kahon Afirka da Sin ta gabatar da shawarar rika gudanarwa tun a shekarar 2022, ya shigar da karsashi ga kokarin shawo kan manyan matsalolin nan uku dake addabar yankin, wato tsaro, da karancin ci gaba da kuma jagoranci na gari.
A nasa bangare kuwa, babban jagoran cibiyar nazarin manufofi samar da ci gaba ta nahiyar Afirka Peter Kagwanja, cewa ya yi kwazon Sin na neman ci gaba ta hanyoyin lumana, ya samar da wani kyakkyawan misali na matakan da kasashen Afirka za su iya aiki da su domin kaucewa fadawa rudani.
Kagwanja ya kara da cewa, kammala aikin layin dogo na SGR da tallafin kudaden gudanarwa daga kasar Sin, wanda ya sada biranen Mombasa da Nairobi, kuma nasararsa ta haifar da bunkasar harkokin tattalin arziki da zamantakewar al’ummun yankin, ya samar da wata dama ta yaukaka zaman lafiya, da dunkulewar sassa daban daban, da ci gaba wanda ya game dukkanin yankin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp