Kwararre a fannin tsara manufofi dan kasar Habasha, Farfesa Costantinos Berhutesfa Costantinos, ya ce hadin gwiwa da kasar Sin ya bunkasa ci gaban kasashen Afirka, yayin da bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka karo na 3 ya kara ingiza saurin ci gaban da nahiyar ke samu.
Yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya bayan nan, Farfesa Costantinos, wanda ke koyarwa a jami’ar Addis Ababan kasar Habasha, ya ce baje kolin wanda ya gudana tsakanin ranaikun Alhamis zuwa Lahadin nan a birnin Changsha fadar mulkin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin, zai karfafa fadadar alakar cinikayya da tattalin arziki tsakanin Sin da kasashen Afirka, tare da kara tabbatar da matsayin kasar Sin, na kasancewa muhimmiyar abokiyar cudanyar kasashen na Afirka.
Baje kolin na bana, mai taken “Ci gaban bai daya domin makomar bai daya ga kowa” ya samu halartar wakilai daga kasashen Afirka 53, da wasu hukumomin kasa da kasa da dama. Kaza lika adadin masu baje hajoji yayin baje kolin na bana ya kai 1,500, adadin da ya karu da kaso 70 bisa dari kan wanda ya gabace shi.
A cewar shaihun malamin, yanzu haka, kasar Sin ce abokiyar cinikayyar Afirka mafi girma, kuma kasa ta hudu a girman zuba jari a nahiyar. Har ila yau, alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2022, cudanyar cinikayya tsakanin Sin da kasashen nahiyar ta kai darajar dalar Amurka biliyan 282. Kuma cikin watanni hudun farkon shekarar nan, adadin sabbin kudaden jarin kai tsaye da Sin ta zuba a kasashen Afirka ya kai dala biliyan 1.38, adadin da ya karu da kaso 24 bisa dari a shekara.
A daya bangaren kuma, tasirin Sin a fannin bunkasar tattalin arzikin kasashen Afirka, ya wuce batun samar da ababen more rayuwa, inda ya kutsa zuwa sauran muhimman fannonin samar da ci gaba. Gina yankunan raya tattalin arziki na musamman da Sin ta yi a kasashen nahiyar da dama, shi ma ya samar da karin damar bunkasa fannin masana’antun nahiyar Afirka.
Farfesa Costantinos ya kara da cewa, kasashen Afirka da kamfanonin su, za su iya cin karin gajiya daga baje kolin, musamman a fannin bunkasa ayyukan masana’antu, ta yadda za su kara shiga kasuwannin Sin, da ma na sauran sassan duniya. (Saminu Alhassan)