• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Gwiwa Tsakanin Matasan Sin Da Afirka Zai Fadada Cin Gajiyar Kasashen Su

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Bayan kammalar dandalin matasan Sin da Afirka karo na biyu da aka gudanar a ‘yan kwanakin baya ta kafar bidiyo, masana da masu fashin baki sun nuna gamsuwa da ma’anar dandalin, bisa yadda aka yi amfani da shi wajen yin kira da a karfafa kawance, da hadin gwiwa a fannoni daban daban, domin raya Sin da Afirka bisa juriya da cin moriyar juna yadda ya kamata.

Dandalin wanda kungiyar sada zumunta tsakanin jama’ar kasar Sin da ta kasashen waje ko CPAFFC ta shirya, ya hallara masu ruwa da tsaki a fannin tsara manufofi, da ma’aikatan diflomasiyya, da masana, da dalibai, da wakilai daga kungiyoyin lura da walwalar jama’a, ya jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwa tsakanin matasan Sin da na kasashen Afirka, a matsayin wani ginshiki na kyautata rayuwar bil adama.

  • Xi Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Ilimi Karo Na 16 Na Cibiyoyin Kimiya Na Kasashe Masu Tasowa

Wanda kuma nasarar sa za ta bude wani sabon babin goyon bayan juna tsakanin Sin da kasashen Afirka, musamman da yake batu ake yi na matasa, wadanda Bahaushe kan ce da su “Manyan Gobe”.
Alal hakika, Sin da kasashen Afirka, sun jima suna raya kawance da goyon bayan juna a lokutan yalwa da na tunkarar wahalhalu, kuma a matsayin ta na babbar kasa mai tasowa, Sin bata taba mantawa da abokan huldar ta na kasashen Afirka ba, inda take samar musu da tallafi ciki har da na kiwon lafiya, tare da taimakon samar da manyan ababen more rayuwa, kamar layukan dogo, da manyan hanyoyin mota, da gadoji, da cibiyoyin samar da lantarki, da filayen jiragen sama da sauran su.

La’akari da hakan ne ma, masana da dama ke ganin ko shakka ba bu, idan aka yi amfani da dandalin matasan Sin da Afirka, wajen yaukaka dangantakar sassan biyu, hakan zai kara ingiza cimma manyan nasarori a fannoni daban daban tsakanin sassan biyu, musamman ganin cewa, tuni an samar da manyan manufofin bunkasa hadin gwiwar sassan biyu, karkashin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka, da shawarar nan ta “Ziri Daya Da hanya Daya”.

Don haka dai, akwai bukatar matasan Sin da na kasashen Afirka su kara wucewa gaba wajen fadada kawance, da musaya, da hadin gwiwa tsakanin su, domin cimma kafuwar al’umma guda ta Sin da Afirka, mai makomar bai daya a dukkanin fannoni.

LABARAI MASU NASABA

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo
Daga Birnin Sin

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Next Post
‘Yan Bindiga Sun Bukaci N40m Kudin Fansar Yara 20 Da Suka Sace A Neja

'Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Hanyar Abuja Zuwa Kogi

LABARAI MASU NASABA

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

Yaduwar Juyin Mulki A Afirka

November 7, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Hanyoyin Noma Na Gargajiya Ba Za Su Iya Wadata Abinci A Nijeriya Ba -Masanin Kimiyya

November 7, 2025
An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

Sin Ta Kadammar Da Babban Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yaki Na CNS Fujian a Rundunar Sojan Ruwanta

November 7, 2025
Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

Xi Jinping Ya Taya Paul Biya Murnar Tazarce a Kamaru

November 7, 2025
Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

Dantsoho Ya Matsar Da Aikin Tashoshin Apapa Da Tin Can Zuwa Zango Na 1 Na 2026

November 7, 2025
An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano

November 7, 2025

Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho

November 7, 2025
Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.