Duniyarmu na fuskantar matsalolin da suka hada da yake-yake, da rashin tsaro, da koma bayan tattalin arziki, da karancin abinci, da annoba.
Wannan yanayi ya sa ake bukatar wani mataki da zai taimaka wajen saukaka yanayin da ake ciki da raya duniyarmu.
To ko hadin gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin, zai iya biyan bukatunmu a wannan fanni?
An gudanar da taron kolin masu tsara aiwatar da ayyukan da suka biyo bayan taron ministoci na 8, na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) ta kafar bidiyo jiya, inda manyan jami’an bangarorin Afirka da Sin, suka gabatar da hadaddiyar sanarwa da jawabai, wadanda suka nuna yadda hadin gwiwar bangarorin 2 ke taimakawa raya duniyar mu, musamman ta fannoni 2 dake kasa:
Da farko, hadin kan Afirka da Sin, ya sa ana samun hakikanin ci gaba.
An gudanar da taron ministoci na 8 na dandalin FOCAC a kasar Senegal, fiye da watanni 8 da suka wuce. Sai dai yaya ake aiwatar da yarjeniyoyin da aka cimma wajen taron?
A taro na wannan karo, an yi bayani kan wasu nasarorin da aka samu: Cikin fiye da watanni 8 da suka wuce, kamfanonin kasar Sin sun kammala ayyukan gina wasu manyan kayayyakin more rayuwa a kasashen Afirka, da suka hada da babbar gadar Fanggioni ta kasar Senegal, da tagwayen hanyoyi dake dab da filin jiragen sama na kasar Kenya, da babbar hanyar mota ta Kribi-Lolabe dake kasar Kamaru, da dai sauransu. Kana cikin watanni 7 da wuka wuce, kasar Sin ta shigo da kayayyaki masu darajar dala biliyan 70.6 daga kasashen Afirka, da zuba dala biliyan 2.17 ga kasuwannin Afirka.
Ban da wannan kuma, an tanadi ayyukan da za a gudanar da su kamar haka: kasar Sin za ta yafe wa wasu kasashe 17 dake nahiyar Afirka bashin da take binsu, da samar da karin tallafin abinci ga wasu kasashen da suke da bukata, da kara jiragen sama masu daukar fasinjoji, da suke zirga-zirga tsakanin Afirka da Sin, da dai sauransu.
Duk wata yarjejeniyar da aka kulla a baya, za a aiwatar da ita. Sa’an nan a yi cikakken bayani kan shirin da za a gudanar, don tabbatar da cika alkawuran. Wannan ya nuna yadda ake hadin gwiwa tsakanin Afirka da Sin don neman hakikanin ci gaba.
Sa’an nan, fanni na biyu shi ne, hadin gwiwar Afirka da Sin, a bude yake ga sauran bangarori.
Shin ko kasar Sin tana yin hadin gwiwa da kasashen Afirka don neman shawo kansu, da samun moriyar siyasa? Batun ba haka yake ba. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana a wajen taron jiya cewa, “ Kasar Sin na son ganin gamayyar kasa da kasa sun ci gaba da mai da hankali kan kasashen Afirka, da nuna musu goyon baya.
Idan kasashen Afirka sun yarda, za a iya yin hadin kai tsakanin bangarori 3 ko fiye, a nahiyar Afirka. Kasashen Afirka suna bukatar wani yanayi na kwanciyar hankali da sada zumunta, maimakon ra’ayin yakin cacar baka, kana suna maraba da hadin gwiwar da zai amfani jama’a, maimakon shiga takarar wasu manyan kasashe.” Wannan magana ta nuna yadda bangaren Sin ke fahimtar ra’ayin kasashen Afirka.
Ta hanyar yin bincike kan tarihin hadin gwiwar Sin da Afirka, za mu iya fahimtar cewa, kasashen Afirka da kasar Sin, sun yi watsi da tunani na yakin cacar baka, wanda har yanzu kasashen yamma suke tsayawa a kai.
Sa’an nan sun juya ga tunanin al’ummar dan Adam mai makomar bai daya. Wanne ne daga cikin su zai fi amfanar al’ummun duniya?
Na san kowa zai iya ba da amsa.
Magance sabanin ra’ayi, da neman cimma matsaya, da kokarin hadin gwiwa don daidaita matsalolin da ake fuskanta, da neman samun hakikanin ci gaba, wannan shi ne ra’ayin da zai iya taimakawa, wajen kyautata yanayin da duniyarmu ke ciki, kuma babbar manufa ce da kasashen Afirka da kasar Sin ke tsayawa a kai, yayin da suke hadin gwiwa da juna. (Bello Wang)