Tsohon jakadan kasar Ghana dake kasar Sin Anani Okuminyi Demuyakor, ya bayyana wa ‘yan jaridar kamfanin dillancin labaru na Xinhua a kwanakin baya a birnin Accra, babban birnin kasar cewa, a cikin shekaru da dama da suka gabata, an raya hadin gwiwar dake tsakanin Ghana da Sin a fannoni daban daban, wanda hakan ya kawo babbar moriya ga kasashen biyu.
Jakada Demuyakor ya bayyana cewa, a cikin shekaru fiye da 60 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Ghana da Sin, an raya dangantakarsu, da hadin gwiwarsu a fannoni daban daban.
Tare da fadada yawan cinikin dake tsakanin kasashen biyu a shekarun baya-baya nan, kuma Ghana ta riga ta kasance daya daga cikin muhimman kasashe abokan hadin gwiwar cinikayya da kasar Sin a nahiyar Afirka.
Tsohon Jakadan ya ce, bayan kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Ghana da Sin, ya lura da nasarorin da Sin ta samu, bayan da ta bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a gida, tare da bunkasuwar hadin gwiwar dake tsakanin Ghana da Sin. Kuma a fannin gina ayyukan more rayuwa a kasar Ghana, hanyoyin mota, da gadoji, da tasoshin jiragen ruwa, wadanda kamfanonin Sin suka gina sun saukaka harkokin sufuri sosai ga jama’ar kasar.
A ganin Demuyakor, hadin gwiwar dake tsakanin Ghana da Sin yana da kyakkyawar makoma.
A cikin shekarun baya-baya nan, Sin ta samu bunkasuwa cikin sauri a fannin sadarwa, don haka ya dace kasar Ghana ta koyi fasahohin kamfanonin Sin, don inganta karfinsu a wannan fanni. (Zainab)