• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Tattalin Arzikin Dijital Ta Haifar Da Dimbin Sakamako

by CGTN Hausa
1 year ago
Sin

A shekarun baya, manhajojin wayar salula da kamfanonin Sin suka zuba jari cikinsu na kara samun karbuwa a kasar Najeriya. Wani abokina ya taba gaya min cewa, ya kan yi amfani da Opay wajen tura kudi. Ya ce yadda ake amfani da shi na da sauki, saboda kusan babu wata dakatarwa. Sa’an nan wani aboki ya ambaci APP mai suna Boomplay, ya ce ya kan saurari wakoki a kansa, ganin yadda ake samun dimbin wakokin kasashen Afirka a cikin APP din. To, wadannan misalai sun nuna yadda hadin kan kasashen Afirka da kasar Sin ta fuskar tattalin arzikin dijital da ya shafi fasahohin zamani ya zurfafa.

A wajen taron kulla huldar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da ya gudana a Nairobi na kasar Kenya, a kwanakin baya, jami’ar Hunan ta kasar Sin, da cibiyar binciken dabarun habaka hadin kan Sin da Afirka kan tattalin arizki da ciniki, sun gabatar da wani rahoto kan hadin kan Sin da Afirka ta fuskar tattalin arzikin dijital, inda suka yi cikakken bayani kan sakamakon da kasashen Afirka da kasar Sin suka samu, a kokarinsu na hadin gwiwa a fannin tattalin arikin dijital, cikin shekarun nan.

  • Sin Ta Kalubalanci Amurka Da Ta Samar Da Kyakkyawan Yanayin Hadin Gwiwa Kan Tinkarar Sauyin Yanayi Da Kyautata Tsarin Raya Tattalin Arzikin Duniya Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
  • Xi Jinping Ya Nuna Matukar Godiya Ga Mahaifiyarsa

Rahoton ya nuna cewa, a fannin gina kayayyakin more rayuwa masu alaka da tattalin arzikin dijital, kasar Sin ta aiwatar da dimbin ayyuka na shimfida wayoyin sadarwa a karkashin teku, wadanda suka hada nahiyar Afirka da sauran nahiyoyi daban daban. Kana kamfanonin kasar Sin sun gina fiye da rabin tashohin wayar salula na kasashen Afirka.

A fannin samar da APP din wayar salula, dimbin kamfanonin hada-hadar kudi na kasar Sin na samar da hidimomin biyan kudi ta wayar salula, da tura kudi tsakanin kasashe, a nahiyar Afirka. Ban da haka, kamfanin Alibaba na kasar Sin ya yi hadin gwiwa tare da gwamnatin kasar Rwanda wajen kafa wani dandalin ciniki mai taken Afnea, wanda ya zama wani dandalin sarin kananan kayayyaki dake da farin jini a gabashin nahiyar Afirka.

Haka zalika, a fannin kirkiro fasahohi, kamfanin Huawei na kasar Sin ya kafa cibiyar adana alkaluma a kasar Afirka ta Kudu, wadda ta samar da hidimomi masu inganci da tsaro. Yayin da kamfanonin Sin ke hadin kai tare da kasashen Masar da Aljeriya, dai dai sauransu, wajen kafa cibiyar kula da ayyukan taurarin dan Adam ta kasar Sin da kasashen Afirka. Ban da haka, a fannin bayar da horo, Sin da kasashen Afirka sun kafa dimbin dandalin samar da ilimi da musayar fasahohi, karkashin hadin gwiwarsu.

LABARAI MASU NASABA

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

Wadannan abubuwa suna cikin dimbin sakamakon da aka ambata, cikin rahoton da aka gabatar, dangane da hadin gwiwar Sin da Afirka, ta fuskar tattalin arziki na dijital.

Sai dai me ya sa ake samun wannan yanayi mai armashi a hadin gwiwar Sin da Afirka a kokarinsu na raya tattalin arzikin dijital?

Da farko, an samu damar raya tattalin arzikin dijital a kasashen Afirka yanzu.

A fannin manufofi, kungiyar kasashen Afirka AU ta zartas da ajandar aiki ta shekarar 2063, inda ta saka burin mayar da nahiyar Afirka yankin tattalin arzikin dijital mai tsarin bai daya. Kana mambobin kungiyar sun dora muhimmanci kan raya tattalin arzikin dijital a cikin gida. Misali, kasar Najeriya ta tsara shirin kara saurin yanar gizo ko Internet, da sanya ta shafar karin mutane. Ban da haka, a fannin muhallin kasuwanci, habakar biranen kasashen Afirka cikin sauri ta samar da kasuwanni ga hidimomi na dijital, kana kafuwar yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka ta ba da damar inganta hadin gwiwar kasashen Afirka ta fuskar tattalin arzikin dijital.

Na biyu, shi ne, fasahohin kasar Sin a fannin yanar gizo su ne a kan gaba a duniya.

An kammala aikin gina kayayyakin more rayuwa masu alaka da fasahohin sadarwa mafi girma a duniya, a kasar ta Sin, ta yadda ko a cikin kauyukan kasar ma, ana samun ingantaccen tsarin sadarwa. Ban da haka, kasar ita ta fara rungumar fasahar sadarwa mai inganci ta 5G, inda a karshen shekarar 2023, yawan al’ummar kasar masu wayoyin salula dake aiki da 5G ya kai miliyan 805. Ban da haka, kasar Sin ta kware a fannin kirkirar sabbin fasahohi, abin da ya sa ta kan gaba a duniya a fannonin mallakar fasahohi masu alaka da na’urorin kwaikwayon tunanin dan Adam, da aikin tsara karamin kayan latironi na Chip, da dai sauransu.

Kana dalili na uku shi ne, akidar kasar Sin ta fuskar hadin kai tare da kasashen Afirka bisa gaskiya, da kauna, da sahihanci, gami da samar da sakamako na zahiri, ta sa kasar yarda da gabatar da ingantattun fasahohi, da damammakin raya kasa, ga bangarorin Afirka.

Cikin shawarar kafa al’umma mai makomar bai daya a fannin yanar gizo bisa hadin gwiwar Sin da Afirka, da kasar Sin ta gabatar, kasar ta yi alkawarin taimakawa kasashen Afirka wajen gina kayayyakin aikin sadarwa, da kula da yanar gizo, da sayar da kayayyaki ga kasuwannin Sin ta hanyar cinikin yanar gizo, da kuma rage talauci ta hanyar amfani da fasahohin zamani, da sauransu.

A lokacin baya, mutane kalilan na kasashen Afirka ne suke da damar duba shafukan yanar gizo ko Internet. Amma zuwa yanzu, ci gaban fasahohi ya sa dimbin mazauna yankunan karkara na nahiyar Afirka na iya kallon shafukan Internet ta wayar salula, don more damammakin sadarwa da samun bayanai. Ta haka za mu iya ganin yadda fasahohin zamani ke haifar da rayuwa mai inganci a nahiyar Afirka. Sa’an nan abun da kasar Sin ke yi yanzu, shi ne kara saurin shigar da ingantattun fasahohi cikin nahiyar Afirka, ta yadda za a ba dukkan bangarorin Sin da Afirka damar amfanar juna, da samun ci gaba na bai daya. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani
Ra'ayi Riga

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

October 28, 2025
Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

October 27, 2025
Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata
Ra'ayi Riga

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

October 23, 2025
Next Post
Sojoji Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Bindiga A Kaduna

Sojoji Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗan Bindiga A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Rikon Kwarya: Shirin DSS Ne Na Damke Atiku Da Peter Obi Kafin Rantsar Da Tinubu

DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta

October 29, 2025
An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

October 29, 2025
Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

October 29, 2025
ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC

October 29, 2025
‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

October 29, 2025
Sanusi Ga ‘Yan Nijeriya: Ku Dora Wa Buhari Alhakin Matsatsin Tattalin Arziki Ba Tinubu Ba

Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II

October 29, 2025
Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

October 28, 2025
JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

JIBWIS Ta Miƙa Takardar Koke Ga Gwamnatin Kaduna Kan Zargin Wasu Malamai Da Yunƙurin Tada Husuma

October 28, 2025
An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu

October 28, 2025
Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal

October 28, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.