Ministan harkokin wajen tarayyar Nijeriya, Yusuf Maitama Tuggar ya ce, “mu baligai ne, kada kasashen yamma su dauke mu a matsayin yara, don muna da ‘yancin zabin abin da muke so.” Ministan ya yi furucin ne a lokacin da yake amsa tambayar wakilin kafar CGTN, a yayin taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) da ya gudana a kwanakin baya a birnin Beijing.
Tabbas kasar Sin ta samu ci gaban a zo a gani a cikin ‘yan shekarun nan, sai dai hakan ya sa wasu mutanen kasashen Amurka da yammacin duniya ba su ji dadi ba, don haka, suka yi ta yayata kalaman wai “Sin barazana ce”, tare da shafa wa kasar bakin fenti kan cewa wai tana kafa “sabon salon mulkin mallaka” a kasashen Afirka da ma jefa kasashen cikin matsalolin basussuka. Amma wadannan mutane sun sha kaye a yunkurinsu na lalata huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka, sabo da ba su san ainihin dalilin da ya sa Sin da kasashen Afirka suke rungumar juna ba.
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Ranar Malamai Ta Kasar Sin
- Nijeriya Ta Samu Lambobin Yabo 7 A Wasannin Nakasassu Ta Bana
A hakika, ba wai cikin ‘yan shekarun nan ne huldar da ke tsakanin Sin da kasahen Afirka ta bunkasa ba. Kasar Sin ta fara taimaka wa kasashen Afirka ne tun a lokacin da ita kanta ke cikin kangin talauci. A farkon shekarun 1970, bayan da kasashe masu ci gaba suka ki taimaka musu, sai Tanzania da Zambia suka juya ga kasar Sin suka roke ta don ta ba da taimakon gina wata layin dogon da zai hada kasashen biyu. Daga baya, magina da injiniyoyi sama da dubu 50 na kasar Sin sun yi iyakacin kokarin kammala wannan aikin da a bakin kasashen yamma abu ne da ba zai yiwu ba, matakin da ya samar da muhimmin taimako ga kasashen biyu da ba da jimawa ba suka samu ‘yancin kansu wajen tabbatar da dogaro da kai ta fannin tattalin arziki. A kuma cikin shekarun 1970, kasashen Afirka ne suka ba da muhimmin taimako wajen maido da kujerar kasar Sin a MDD, wadanda suka tsaya tare da kasar Sin wajen kiyaye halastacciyar moriyarta a duniya.
Sin da kasashen Afirka sun fara kulla abota ne a lokacin da suke gwagwarmayyar neman ‘yancin kansu, wadda ta kara bunkasa a lokacin da suke kokarin neman ci gabansu. Da aka shiga sabon karni na 21, bisa tsarin dandalin FOCAC da ma shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, kasar Sin ta taimaka wa kasashen Afirka gina ko gyara hanyoyin mota da tsawonsu ya kai kusan kilomita dubu 100, da ma layukan dogo sama da kilomita dubu 10, sai kuma gadoji kusan dubu da tashoshin jiragen ruwa kusan 100…A sa’i daya kuma, kasashen Afirka ma sun yi kokarin ba wa kasar Sin taimako gwargwadon karfinsu. Ba za mu taba mantawa ba, a lokacin da mummunar girgizar kasa ta afkawa gundumar Wenchuan ta kasar Sin a shekarar 2008, kasar Equatorial Guinea ta samar wa kasar Sin gudummawar kudin Euro miliyan guda, daga baya, ta kuma samar da miliyoyin daloli na gina wata makarantar firamare a lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin.
Yanzu haka, kasar Sin na kokarin zamanintar da kanta, kuma zamanintar da kansu buri ne na bai daya ga kasashen Afirka. A gun taron kolin FOCAC na wannan karo, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da wasu shirye-shiryen kawance guda 10 da ake son aiwatarwa tare da kasashen Afirka nan da shekaru uku masu zuwa a kokarin zamanintar da kansu, shirye-shiryen da suka shafi fannoni 10 da suka hada da musayar al’adu da hada-hadar cinikayya da hadin gwiwar tsarin masana’antu da hadewa da juna da sauransu. Domin aiwatar da shirye-shiryen, gwamnatin kasar Sin za ta kuma samar da tallafin kudi da yawansa ya kai yuan biliyan 360 nan da shekaru uku masu zuwa. A cewar shugaba Xi Jinping, “Ba za a bar kowace kasa a baya ba a kokarin da ake yi na zamanintar da kai.”
Makomar Sin da kasashen Afirka daya ce a kullum, makamantan abubuwan da suka faru gare su a tarihi da ma burinsu na bai daya ya hada su tare, daidai kamar yadda karin magana na Afirka ya bayyana, wadanda ke bin hanya daya su ne abokai na gaske.
A gun taron kolin, shugaban tarayyar Nijeriya ya ce, hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da ke cike da nasarori ya shaida cewa, ba lallai ba ne a ci nasara daga faduwar wani bangare a yayin da kasa da kasa ke neman ci gabansu. Abin haka yake, a zamanin da muke ciki na dunkulewar tattalin arzikin duniya, kasa da kasa sun kasance suna cude-ni-in-cude-ka, kuma duniyarmu na da girman da ya ishi kasa da kasa su samu ci gaba tare, ba sai an ci nasara daga faduwar wani bangare ba.
A yayin da huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka ke dada bunkasa, karin kasashe na mai da hankalinsu a kan Afirka, hakan ya sa kasar Sin matukar farin ciki. Kasar Sin na maraba da kasa da kasa da su kara ba wa kasashen Afirka goyon baya da kuma taimaka musu, sabo da ci gaban dan Adam ba ya iya rabuwa da ci gaban kasashen Afirka, kuma idan ba a kai ga zamanintar da kasashen Afirka ba, to, ba maganar zamanintarwar duniya ke nan.(Lubabatu Lei)