Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce matakin tsawaita yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka, a fannonin kimiyya da fasasha ya yi daidai da moriyar al’ummunsu, kana ya dace da burin sassan kasa da kasa.
Lin Jian wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan, yayin taron manema labarai, lokacin da yake amsa tambaya mai nasaba da batun, ya ce, Sin da Amurka sun sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita hadin gwiwar ne a ranar Juma’a, zuwa karin shekaru 5, tun daga ranar 27 ga watan Agustan shekarar nan ta 2024, kamar dai yadda ma’aikatar kimiyya da fasaha ta Sin ta tabbatar.
Jami’in ya ce, muhimmancin wannan yarjejeniya, shi ne cimma moriyar bai daya, da tabbatar da cin gajiyar sassan biyu tare. Kaza lika, tsawaita wa’adin muhimmin mataki ne na cimma nasarar aiwatar da kudurorin da shugabannin kasashen 2 suka cimma matsaya a kansu, kuma hakan zai ingiza ci gaban kimiyya da fasaha, da bunkasa harkokin tattalin arziki da zamantakewar al’ummun kasashen 2, baya ga taimakawa wajen shawo kan tarin kalubalen dake gabansu, da kyautata yanayin rayuwar al’ummun dake mabambantan sassan duniya. (Saminu Alhassan)