Assalamu alaikum barkammu da sake haduwa a wannan makon a cikin shirin namu na Girki Adon Mata.
A wannan makon za mu kawo muku kayataccen girkimmu mai suna Ijjah:
- Da Dumi-Dumi: INEC Ta Dage Zaben Sanatan Enugu Ta Gabas
- Gwamnatin Tarayya Da Jihohi Da Kananan Hukumomi Sun Kasafta Naira Biliyan 750.17 A Janairu
Ijjah dai wani soyayyan abinci ne mai dandano wanda a ke cinsa kamar lokacin karya kumullo wato da safe (Breakfast).
Abubuwan da ya kamata Uwargida ta tanada domin hada Ijjah:
Fasili, koren Tattasai, Albasa, Attaruhu, Magi da Gishiri, Kuri, Fulawa, Kwai, Mai.
Yadda Uwargida Za Ki Hada Ijjah Dinki:
Da farko za ki sayo fasili a wajen masu saida ganyayyaki kamar uguh da Alayyahu masu saida wadannan ne suke sai da shi za ki ganshi kananu ne idan ki ka sayo sai ki tsittsige shi kamar yadda za ki cire alayyahu, sannan ki yayyanka shi ki wanke shi da gishiri sannan ki zuba shi a kwalan da saboda ya tsame ruwan jikinsa sai ki ajiye shi a gefe sannan ki dauko koran tattasanki shima ki yayyanka shi amma kanana sannan ki yayyanka Albasa ita ma kanana, sai ki jajjaga attaruhunki bayan kin jajjaga sai ki zuba shi a kan wannan fasili din sai ki dakko magi ki zuba a ciki da kori da dan gishiri, sannan sai ki dakko kwai ki fasa a ciki idan kika fasa kwai za ki ga kamar ya danyi ruwa-ruwa kin ga kin sa kwai sai ki dakko fulawa ki daure shi, amma kar ya yi tauri da yawa ya yi dan ruwa ruwa kamar dai kullun kosai yadda idan kika zuba shi zai kame jikinsa.
Sannan kuma ba zai sha miki mai ba sannan sai ki dora manki a wuta idan ya yi zafi sai ki dinga diba da cokali kina zubawa kamar yadda ake zuba kosai amma shi ba ya son wuta da yawa za ki sa wuta ba da yawa ba, sannan kuma ba kadan ba saboda idan wuta ta yi masa yawa cikin ba zai soyo ba, sannan kuma idan wuta ta yi masa kadan zai sha mai idan ya soyo za ki ga ya yi ruwan kasa, sai ki juya shi saboda samansa ma ya yi.
Shi wannan Ijjah ana cinsa da kunu ko custand ko shayi da dai sauransu a ci dadi lafiya ba’a ba wa yaro maran kiwa.