Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.
Shafin namu zai ci gaba da bayani a kan yadda ake hadin sabulu na musamman kamar yadda muka faro a makon da ya gabata.
- Sin Na Fatan Amurka Za Ta Martaba Ikon Mulkin Kai Tsaro Da Moriyar Ci Gabanta
- Hajjin 2024: Abubuwan Da Suka Kamata A Sani
Sabulu na musamman
Kayan Hadi:
Madarar Turare, lalle Da Dilka, Ganyen Magarya, Kurkur, Dudu Osun Da Detol, Sabulun Ghana:
Yadda za ki hada:
A hada su wuri daya a daka su a turmi mai kyau su hade jikinsu sosai sai ki rinka wanka da shi. Yana da kyau sosai.
Sabulun wanka na Ghana:
Kayan hadi:
Kur-Kur, Dilka, Zuma Kwai, Lemon Tsami
Yadda za ki hada:
Za ki hade su a guri guda ki samu ruwa ki kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma ya fi kwabin lallen ruwa, sai ki shafe fuskanki, idan kuma har da jiki kike so, sai ki shafa har da jikin bayan awa daya sai ki shiga wanka za ki ga yadda jikinki zai goge tas da izinin Allah. Domin wannna hadin shi ake kira Dalleliya.
Ga kuma wani hadin, shima na gyaran fatan jiki za ki tanadi:
Lalle, kwaiduwar kwai 3, manja cokali 3, Kur-kur.
Sai ki kwaba su guri guda ki shafe jikinki zuwa awa guda, sai ki yi wanka da ruwa zalla sai ki jika duka da ruwan dumi ki shafe jikin da ita sai ki kuma yin wanka. Allah ya taimake mu.
Domin samun laushin fuska kuma:
Za ki shanya bawon lemon zaki da na kwai sai ki daka su yi laushi ki kwaba da ruwa ki rika shafawa kafin ki shiga wanka.
Gyaran Fuska:
Tumatir, Madara; ki kwaba madara da tumatir sai ki shafa tsawon minti 30 sai ki wanke.
Garin Alkama, Zuma, Madara; ki hada su ki rinka shafawa kafin ki shiga wanka
Lemon tsami, zuma. Ki hada su idan za ki kwanta ki rinka shafawa da safe ki wanke da ruwan dumi
Ki samu Man Ridi, Man Kwakwa, Man Habba, Miski; ki hada mayukan sai ki diga turaren miski ki rinka shafawa yana sanya fata ta yi laushi da santsi
Man shafawa don laushin jiki: Man Kwakwa, Man Kade, Man Angurya, Man Daitun, Almond Oil,Baby Oil, Madarar Turare, Cocoa Buter; Ki hada su duka ki rika shafawa jikinki zai yi taushi sannan ki hada da sabulun sabulun Zaitun, Tetmasol, Sabulun Salo da Ghana, Sabulun Karas, Sabulun Cocumber, Kurkur. Ki hada su ki rika wanka da su amma sai an jure. Ko ya kare ki sayo ki sake hadawa sannan ki rage shiga rana.
Domin magance kurajen fuska:
Ruwan Khal, Zuma, Man Zaitun
Za ki dora ruwan Khal da Man Zaitun da zuma a wuta su yi zafi sai ki dan kara ruwa ki juya sosai ki wanke fuskarki, sannan ki nemi auduga ki rika goge fuskarki da hadin musamman wurin kurajen.
Steaming na fuska:
Kayan hadi: Kwai, zuma, nono.
Yadda zaki hada:
ki kwaba su sai ki shafa a fuska sai ki turara da ruwan zafi ya kan hana fitowar kuraje tare da kashe su.
Hasken Fata: Za ki sami itacen Sandal Wood ki daka sai ki kwaba da Kurkur da Madara ki rika shafawa kafin ki yi wanka.
Za ki kwaba Kurkur da Madara tare da Kwaiduwar Kwai kina shafawa kafin wanka safe da yamma.
Za mu ci gaba mako mai zuwa idan llah ya kai mu.