Connect with us

FITATTUN MATA

Hadiza Bala Usman: Jarumar Da Tarihin Ceto ‘Yan Matan Chibok Ba Zai Manta Da Ita Ba  

Published

on

Ko-kun-san?

Hadiza Bala Usman ita ce Darakta Janar ta hukumar kula da tashohin jiragen ruwa a Nijeriya, ta kasance ‘yar gwagwarmayar ‘yanto Matan makarantar Chibok da ‘yan Boko Haram suka yi garkuwa da su. Ta ba da tata gudunmawar sosai wajen neman hanyoyin da suka dace domin lalubo bakin zaren matsalar tare da hada iyayen matan da aka sace da gwamnati domin daidaita lamura a zamanin mulkin shugaban kasa Goodluck Jonathan. Tarihi ba zai ambaci sace ‘yan matan Chibok ba sai ya ambato sunan Hadiza bisa gudunmawar da suka bayar a karkashin kungiyar da suka kafa ta ‘Bring Back Our Girls’. Ta kasance fitacciyar ‘yar siyasa da ta yi jam’iyyar PDP, CPC yanzu haka tana cikin jam’iyyar APC tsundum.

 

Wace Ce Hadiza Bala Usman?

 

An haifi Hadiza Bala Usman ce a ranar 2 ga watan Janairun 1976 a birnin Zaria ta jihar Kaduna. Ta fara karatun Firamare dinta a makarantar Jami’ar ABU ta kuma yi sakandari. A shekarar 1996 ta shiga Jami’a inda ta samu shaidar kammala Digiri a shekarar 2000, ta karanci fannin gudanar da kasuwanci. Daga baya kuma ta garzaya ta samu digiri na biyu Jami’ar Leeds a shekarar 2009.

 

Mahaifinta Alhaji Yusufu Bala Usman shahararren mai ilimi ne kuma mai cikakken tarihi da ya sanu sosai. Ya kasance shine ya kafa cibiyar ‘Centre for Democratic Debelopment, Research and Training da ke Zariya’. Kakanta na bangaren mahaifiya, shine Abdullahi Bayero da ya kasance Sarkin Kano na 10 a tsakanin 1926 zuwa 1953.

 

Ta yi aiki a Bureau of Public Enterprises a watan July 2000 zuwa Agustan 2004 a matsayin Jami’ar kasuwanci. A watan Oktoban 2004 zuwa Junairun 2008 ta kasance babban mai taimaka wa Minista kan aiwatar da aiyuka.

 

A zaben 2011 da aka gudanar Hadiza ta tsunduma takarar siyasa a mazabar Musawa/Matazu a majalisar wakilai ta kasa karkashin jam’iyyar CPC amma Allah bai bata nasara ba. Daga baya kuma ta shiga kungiyar tabbatar da kyakkyawar shugabanci a Nijeriya GGG inda ta kasace Daraktan tsare-tsare daga 2011 zuwa watan July 2015.

 

Gwagwarmayarta Kan Ceto ‘Yan Matan Chibok:

 

A shekarar 2014 bayan sace ‘yan matan garin Chibok da ‘yan Boko Haram suka yi, Hadiza Bala Usman tana daga cikin jaruman matan da suka kafa kungiyar Bring Back Our Girls domin gangamin wayar da kai da neman ‘yanto matan da aka yi garkuwa da su. Hadiza ta zabi launin Ja a matsayin alamin gangamin neman ceto ‘yan matan a saboda alamin na nuna hadari, ankararwa da kuma gargadi. Bala Usmnan ta taimaka sosai wajen tsarawa da hada taron ganawa a tsakanin iyayen matan da aka sace da jami’an gwamnati domin tattaunawa kan yadda za a samu nasarar ‘yanto ‘yan matan na Chibok. Ta ci gaba da zanga-zanga da neman ‘yanto daliban har zuwa shekarar 2016.

 

A 2015 kuma bayan da aka zabi Nasiru Ahmad el-Rufai a matsayin gwamnan jihar Kaduna, ya nadata a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Kaduna. A watan July na shekarar 2016 ne kuma shugaban kasa Muhammad Buhari ya nada Hadiza Bala a matsayin  Darakta Janar na hukumar kula da tashohin jirgin ruwa a Nijeriya (NPA) lura da cancantarta da cewarta har zuwa yanzu kuma ita ce take jan ragamar wannan hukumar da bincike ya tabbatar da cewar ta taka rawa sosai wajen inganta hukumar da kuma aiki, ta fito da tsare-tsare masu kyau da yanzu haka ake amfana da su wajen inganta harkokin tashoshin jirgin ruwa a kasar nan.

 

Hadiza Bala Usman ta auri wani masani kuma mai sharhi kan tattalin arziki Tanimu Yakubu Kurfi wanda yayi aiki a karkashin tsohon shugaban kasa Ummaru Musa Yar’adua a matsayin mai bashi shawara kan tattalin arziki. Allah ya azurtasu da yara biyu

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: