Haruddan jirgin sama sun sha faruwa a Nijeriya inda suka yi sanadiyar mutuwar mutane da yawa, a cikinsu ga goma wadanda suka fi muni.
- Ranar 20 ga Nuwamba 1969 mutane 87 suka rasa rayukansu a hadarin jirgin sama na Bickers BC-10 wanda ya fadi a Legas Nijeriya.BC-10 ya taso ne daga Landan zuwa Legas inda ya yada zango Rome da Kano.Lokacin da ya kusa isowa Legas sai jirgin ya yi kasa sosai ba kamar yadda aka saba ba ya bugi itace wanda hakan ya sa ya fadi ya kama da wuta.
- Ranar 22 ga Janairu 1973 jirgin sama mai kirar Boeing 707 wanda hukumar jiragen sama ta Nijeriya ta ba shi aiki domin ya maido da Alhazai daga Jidda zuwa Legas ya fadi a Kano ya kashe mutane 176.
Saboda rashi kyawon yanayi a Legas sai aka juya akalar jirgin zuwa Kano.Ya yi yunkurin sauka a titin da jirage ke bi domin sauka amma sai aka samu matsala sai an yi sa’ar ceto ma’aikata biyu da fasinjoji 23 da ransu.
3.11 ga watan Yuli 1991 mutane 261 sun rasa rayukansu lokacin da jirgin sama na McDonnell-Douglas DC-8 da yake dawowa da Alhazan Sakkwato da aikin Hajji a madadin tsohuwar hukumar kula da jiragen sama ta kasa ya fadi a Jeddah, Saudi Arebiya,shine hadari mafi muni a tarihin hadarin jirgin sama a Nijeriya.
Jirgin saman Nijeriya ya taso daga Jedda amma bayan tasowar tsakanin kafa 2000-3000, sai aka samu matsala wadda ma’aikata suka bayyana.
An dauki mataki ba tare da bata lokaci ba sai dai bai hana abin da zai faru ya auku ba domin kuwa an samu matsalar birki wadda ta sa jirgin ya rasa irin halin da yake ciki sai ya fadi ya kama da wuta lokacin da yake kokarin dawowa.Shine hadarin jirgi mafi muni wanda ya shafi jirgin sama mai kirar DC-8 shine kuma hadari na biyu da ya faru a Saudi Arebiya a wancan lokacin.Matsalar da tasa hadarin an dora ta akan kuskure na mutum a hukumar kula da harkokin jiragen sama.
- Ranar 26 ga Satumba 1992 mutane 158 suka mutu wadanda suke cikin jirgin Lockheed C-130H Hercules wanda sojojin saman a kasa ke amfani da shi ya fadi kusa da Legas.
Bayan jirgin ya tashi sai inji na farko ya lalace daganan sai na biyu shi ma ya biyo sahu bada dadewa ba.Ma’aikatan jirgin sun yi kokari su maida akalar jirgin zuwa Ejigbo amma sai inji na uku shi ma ya daina aiki.
Daga karshe dai jirgin ya fada a wurin da ruwa yake mai tabo ba a san ko mutane nawa bane suka mutu.Akwai ‘yan Nijeriya a kalla 150, ‘yan kasar Ghana 5,dan kasar Tanzaniya 1, dan Zimbabwean 1, da kuma dan Uganda 1 a cikin hadarin.
- Ranar 7 ga Nuwamba 1996 jimillar mutane 144 sun mutu bayan jirgin sama na Boeing 727 da kamfanin jirgin sama na ADC ke amfani da shi ya taso daga Fatakwal zukka Legas ya fadi a Ejirin a inda duk mutanen da ke cikin jirgin suka mutu.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa