Shugaban Rundunar Sojin Nijeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya gana da shugabannin al’umma a Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato, bayan hare-haren da aka kai wasu Æ™auyuka da suka yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 50, tare da rushe gidaje sama da 300, tare da raba sama da mutane 1,000 da muhallansu.Â
Ƙauyukan da lamarin ya shafa sun haɗa da Hurti, Ruwi, Josho, Daffo, Manguna da wasu da ke maƙwabtaka da su.
- Harin Filato: An kashe Mutane 40, An Kona Gidaje 383, Fiye Da Mutane 1,000 An Raba Su Da MuhallansuÂ
- Sabon Tsarin Harajin Kwastam Na Amurka Ya Kwace ‘Yancin Sauran Kasashe
A wajen taron, Laftanar Janar Oluyede ya buƙaci al’ummar yankin da su rungumi zaman lafiya da haɗin kai.
Ya ce dole ne a yi aiki tare domin samun zaman lafiya, ba wai a bar komai a hannun sojoji kaÉ—ai ba.
Ya kuma tabbatar da cewa sojojin Nijeriya za su ci gaba da zama masu adalci da kare kowa ba tare da nuna bambancin ƙabilanci ko addini ba.
Shugaban sojin ya ce za a kamo waɗanda suka aikata wannan mummunan ta’asa, kuma za a hukunta su.
Haka kuma ya yi alƙawarin tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa domin kare rayuka da dukiyoyi.
A nasa jawabin, Manjo Janar Folusho Oyinlola, kwamandan Operation Safe Haven, ya ce za su ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya musamman a lokacin girbin gonaki.
Ya bayyana cewa ganawar da shugabannin yankin na zuwa a lokaci mai muhimmanci duba da yadda matsalar tsaro ke ƙaruwa.
Dagacin Manguna, Alhaji Alo Raymond, ya ce hare-haren da ake kai musu na da nasaba da yunƙurin karɓe musu filayen gado.
Ya roƙi gwamnati ta kare su da gidajensu, tare da tallafa wa waɗanda abin ya shafa da abinci da sauran kayan buƙatu domin farfaɗo da rayuwarsu.
Wasu daga cikin mazauna yankin da suka halarci taron sun bayyana fatan cewa wannan ziyara da kuma alƙawuran da shugabannin tsaro suka yi za su haifar da zaman lafiya.
Sun kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta jiha da su ɗauki mataki gaggawa domin kawo ƙarshen wannan rikici da kuma tallafa wa waɗanda suka rasa matsugunnai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp