A ranar Litinin 10 ga watan nan ne aka bude bikin baje-kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa na kasar Sin, karo na 3 a birnin Haikou na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.
Ana sa ran nuna kayayyakin masarufi masu inganci fiye da 3300, daga kasashe da yankuna sama da 60, a yayin bikin da za’a gudanar har zuwa ranar 15 ga wata. Baje kolin ya yi maraba da mahalartan sa da ce “A zo Hainan, a sayi kayayyakin kasa da kasa, tare da sayar da kayayyaki zuwa ga duk duniya!”, inda lardin Hainan, wato yankin cinikayya maras shinge mafi girma a kasar Sin, ya shaida yadda kasar take himmatuwa wajen zurfafa yin kwaskwarima a gida tare da bude kofar ta ga kasashen waje daga dukkanin fannoni.
A wajen zama na farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 7, wanda aka gudanar shekaru 35 da suka gabata, an amince da kafa lardin Hainan, da ayyana tsibirin Hainan din a matsayin yankin tattalin arziki na musamman.
A ziyarar aikin da ya yi a Hainan a shekara ta 2018, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya halarci gagarumin bikin cika shekaru 30 da kafa lardin, tare da yankin tattalin arziki na musamman a Hainan din, inda ya gabatar da muhimmin jawabin dake jaddada cewa, ya zama dole a raya Hainan, har ya zama sabuwar alkibla ga aikin zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a sabon zamanin da muke ciki. Kana, shugaba Xi ya sanar da wata muhimmiyar shawara cewa, kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin, ya yanke kudurin goyon-bayan raya tsibirin Hainan, har ya zama yankin gwaji na gudanar da cinikayya cikin ‘yanci, da mara masa baya don gina tashar cinikayya cikin ‘yanci mai salon musamman irin na kasar Sin, da tsara manufofi, da tsare-tsaren gina tashar cinikayya cikin ‘yanci mataki mataki.
Tun daga gina yankin tattalin arziki na musamman, zuwa gina yankin gwaji na gudanar da cinikayya cikin ‘yanci, har zuwa gina tashar cinikayya cikin ‘yancin mai salon musamman irin ta kasar ta Sin, Hainan, ya shaida manufar da kasar Sin ke tsayawa a kai, ta kara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. (Murtala Zhang)