Hajiya Safara’u Umaru Barebari, mahaifiyar gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa ta rasu.
Ta rasu tana da shekaru 93 a duniya.
- Ko Raunin ‘Yan Wasa Zai Rage Wa Barcelona Karsashi A Kakar Bana?
- EFCC Ta Cafke Mutum 21 Bisa Zarginsu Da Zambar Intanet A Bauchi
Hajiya Safare, mace ce mai daraja kuma jigo a gidan Umaru Radda, ta rasu ta bar ‘ya’yanta da suka hada da Gwamna Radda, Alhaji Kabir Umar Radda, Hajiya Indo Umar, da Hajiya Hauwa Umar Radda da dai sauransu.
Ana sa ran, za a yi jana’izarta yau Lahadi 23 ga watan Maris, 2025 kamar yadda addinin Musulunci ya tanada da misalin 4 na yamma (4pm) a garin Radda, ƙaramar hukumar Charanchi da ke jihar Katsina.
Hajiya Radda, jigo ce da za a rika tunawa da ita bisa hikima da juriya wanda hakan ya yi tasiri matuka ga iyalai da makusantanta.
Allah ya jikan Hajiya Safara’u Umaru Barebari, ya albarkaci zuri’arta, ya sa ta huta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp