Wata Maniyyaciya ‘Yar Nijeriya mai suna Hajiya Aisha Ahmad ta rasu a yau Laraba sakamakon rashin lafiya a kasar Saudiyya.
Aisha Ahmad daga karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa take, ta rasu ne bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya kamar yadda Alhaji Idris Al-makura, babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Nasarawa ya bayyana.
Al-Makura ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN a ranar Laraba a birnin Makkah na kasar Saudiyya cewa marigayiyar ba ta da wata takardar shaidar rashin lafiya kafin tashinta daga Nijeriya zuwa Kasa Mai Tsarki.
“Marigayiyar ta fara rashin lafiya ne kwana biyu da suka gabata a Madina.
“An fara kai ta Asibitin Hukumar Alhazai ta kasa da ke Makkah, sannan daga nan aka kai ta Asibitin Sarki Abdulaziz inda Allah ya karbi rayuwarta a can. An sanar da danginta kan rasuwarta yadda ya kamata.” Inji Al-makura