Jirgin farko na alhazan Nijeriya da suka gudanar da aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya, ya tashi daga kasar zuwa Nijeriya ranar Talata.
Jirgin farko dauke da mahajjata 425 daga jihar Sokoto ya tashi daga filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah da misalin karfe biyu agogon Saudiyya da yammacin yau Talata.
- Hajjin 2023: Gobe Talata Za A Fara Jigilar Alhazan Nijeriya Zuwa Gida
- Hajjin 2023: Alhazan Nijeriya 14 Sun Rasu A Saudiyya A Aikin Hajin Bana
Ana sa ran jirgin zai sauka a filin jirgin saman Sultan Abubakar, Sokoto, da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar 4 ga watan Yuli.
A cewar Goni Sanda, shugaban kwamitin kula da harkokin sufurin jiragen sama na hukumar alhazai ta kasa NAHCON, komawa gida zai kasance kamar tsarin farko na jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki, domin yin adalci wajen gudanar da aikin, yana mai cewa. Ana sa ran kowane mahajjaci da zai yi kwanaki 40 zuwa 43 a kasa mai tsarki kafin a dawo da shi Nijeriya.
Goni ya yi kira ga maniyyata da su kasance cikin tsarin yayin da suke komawa zuwa gida Nijeriya.