Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta samu nasarar jigilar mahajjata 32,549 zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da Hajjin 2025.
Wannan adadi ya kai kusan kashi 79 na jimillar mahajjatan Nijeriya da za su je aikin Hajji a bana.
- ‘Yansanda Sun Kama Matasa 2 Da Ake Zargi Da Satar Mota A Kebbi
- Gwamnan Filato Ya Kafa Kwamiti Don Binciken Hare-Haren Da Ake Kai Wa A Jihar
An fara jigilar ne tun ranar 9 ga watan Mayu, 2025, inda aka yi amfani da jirage 79 zuwa yanzu.
Wasu jihohi kamar Adamawa da Filato sun riga sun kammala jigilar dukkanin mahajjatansu.
Jihohin Bauchi da Gombe suna da saura mahajjata 30 kowanne, kuma ana sa ran za su kammala jigilar a yau.
Jihar Jigawa da Babban Birnin Tarayya su ma za su kammala nasu a yau.
Jihar Kwara na da sauran mahajjata 137 kuma za su tashi a jirgin Max Air a Kano da rana.
Mahajjatan daga Jihar Binuwai za su haɗe da waɗanda ke yankin Kudu maso Kudu domin tafiya tare a jirgi guda da zai tashi a ranar 23 ga watan Mayu, wanda zai zama jirgi na ƙarshe daga wannan yanki.
A cewar Fatima Sanda Usara, Babbar Daraktar Watsa Labarai a NAHCON, ba a soke jirgi ko ɗaya ba tun lda aka fara jigilar maniyyatan.
NAHCON ta gode wa mahajjata da al’ummar Nijeriya baki ɗaya bisa haƙuri, addu’o’i da goyon baya, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da aiki tuƙuru domin ganin an gudanar da aikin Hajji cikin tsari da sauƙi ga kowa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp