Gwamnatin Jihar Zamfara ta mayar wa da kowane mahajjaci daga cikin alhazai 1, 318 da suka yi aikin hajjin bana zuwa kasar Saudiyya Naira dubu 50.
Gwamna Bello Matawallle wanda ya bada umarnin mayar da kudaden, ya umarci hukumar alhazai ta jihar da ta tabbatar da aiwatar da wannan umarni cikin gaggawa.
- 2023: Za A Bai Wa ‘Yan Hijira Damar Kaɗa Kuri’a A Sansanoninsu – INEC
- EFCC Da Sojojin Nijeriya Sun Hada Kai Don Yakar Cin Hanci Da Rashawa Da Yaki Da Ta’addanci
Ya umarci hukumar da ta fara biyan kudin daga nan zuwa ranar Litinin, 12 ga Satumba, 2022 a kowace karamar hukuma 14 na jihar.
Don haka, an shawarci maniyyatan da abin ya shafa da su je karamar hukumar inda suka biya kudinsu domin karbar Naira 50,000 daga ranar Litinin 12 ga Satumba, 2022.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe, ta ce matakin na daya daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke dauka na rage wahalhalun tattalin arziki da ake fuskanta a kasar.
Balarabe, ya ce gwamnati za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace don tallafa wa jama’a don inganta tattalin arzikinsu, jin dadinsu da kuma daukaka darajar rayuwarsu da walwala.