Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bukaci maniyyatan Jihar da su yi wa Najeriya addu’a ta musamman kan samun zaman lafiya a yayin aikin Hajjin bana a kasa mai tsarki.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya gana da kashin farko na maniyyatan Jihar 428 a ranar Asabar.
- Machina Ya Yi Barazanar Daukar Matakin Shari’a Kan Sauya Sunansa Da Ahmad Lawan
- Peter Obi Na LP Ya Zaɓi Doyin Okupe Daga Ogun A Matsayin Mataimakinsa Na Wucin-gadi
Ana sa ran maniyyata 1,303 ne za su gudanar da aikin Hajjin bana daga Jihar Zamfara a Saudiyya.
Matawalle ya ce Zamfara na bukatar addu’a ta musamman don kawo karshen matsalar tsaro da samun zaman lafiya a fadin jihar, don haka ya bukaci maniyyatan Jihar da su gudanar da addu’o’i na musamman.
Sannan ya bukaci da su kasance masu da’a a yayin gudanar da ibadar da ta kai su kasa mai tsarki.
Ya ce gwamnatinsa ta samar da duk wani abun da maniyyatan za su bukata a lokacin zamansu a kasa mai tsarki don gudanar da aikin Hajjin bana.
Zamfara ta tanadar wa maniyyatan maniyyatan sabbin motoci da za su ke jigilarsu daga sansanin Alhazai na Jihar zuwa filin jirgin saman jihar Sakkwato.
Gwamnan ya ce gwamnatin Jihar ta dauki malamai na musamman wanda za su ke taimaka wa maniyyatan yadda za su gudanar da ibadunsu yayin aikin Hajjin.