Hadakar kungiyar masu daukan rahoton ayyukan hajji masu zaman kansu (IHR), ta bukaci hukumar kula da ayyukan hajji na kasa (NAHCON) da na jihohi da su sanar wa maniyyata abun da za su karba a matsayin alawus din yin tafiya.
A wata sanarwa dauke da sanya hannun ko’odinetan kungiyar na kasa, Ibrahim Muhammed, ya ce, hakan ya zama musu dole ne da su jawo hankalin NAHCON da hukumomin hajji na jihohi kan cewa zuwa yanzu kudin kujerar aikin hajji bai nuna adadin kudin da za a bai wa maniyyata a matsayin alawus ba, sabanin yadda aka saba tafiyar da lamuran a shekarun baya.
- Hajjin 2024: NAHCON Ta Rattaba Hannu Da Kamfanonin Jiragen Sama Kan Yarjejeniyar Jigilar Maniyyata
- 2024 Hajj: Karancin Maniyyata Ba Nijeriya Kadai Ya Shafa Ba – NAHCON
“An saba sanar da kudin kujerar aikin hajji da NAHCON ke yi na zuwa ne da tanadin da aka yi na alawus din tafiyar kowani maniyyaci. Hakan na nuni da bai wa kowani maniyyaci damar kimtsawa a ransa kan nawa ne zai amsa ta yadda zai tsara hada-hadar kudin da zai yi amfani da su.
“A misali, a 2023 maniyyata sun biya miliyan 2.9 aka ba su dala 800 na alawus din tafiya. Kudin kujerar aikin hajji ya kunshi kudaden hidindimun cikin gida da na waje ciki har da alawus din tafiya ga maniyyata.
“Hukumar NAHCON da ta shude daga baya ta rage kudin alawus din tafiya aikin hajjin 2023 zuwa dala 700, bisa abun da ta kira bambance-bambancen farashin kudin jirgi. Amma a aikin hajji na bana tun lokacin da aka sanar da kudin kujerar ba a bayyana nawa ne kudin alawus din ba, har ma zuwa lokacin da aka kara kudin kujerar ba a bayyana nawa ne alawus din matafiyan ba.”
Kungiyar ta ce alawus din tafiyar da ake bai wa alhazai a ranar da suka sauka a kasar Saudiyya na taimaka musu wajen irin sanin abubuwan da za yi da yadda za su kashe kudadensu har ma su samu damar yin guzuri.
Don haka kungiyar ta yi kira ga babban murya ga masu ruwa da tsaki a aikin hajji da su gaggauta sanar da nawa ne alawus din da kowani maniyyaci zai amsa domin ba su damar sanin irin tsare-tsaren da ya dace su yi.