Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta kaddamar da kwamitin tantance kamfanonin jiragen saman fasinja da na dakon kaya don aikin hajjin 2024.
Kamfanonin jiragen fasinja tara da na dakon kaya hudu ne su ka mika bukatar hidima ga alhazan Nijeriya domin aikin hajjin 2024.
- Matakan Amurka Na Kayyade Fitar Da Matattarar Bayanai Ta Microchip Za Su Kawo Illa Ga Kasuwar Samar Da Kayan Ta Duniya
- ‘Yansanda Sun Kama Darakta Da Wasu Mutane 2 Bisa Zargin Gwanjon Kayan Gwamnatin Kano
Shugaban NAHCON Malam Jalal Ahmed Arabi, ne ya kaddamar kwamitoci biyu; masu wakilai 32 domin tantancewa da su.
Jalal Arabi ya ce duk abin da a ke so a yi nasara to tabbas sai an fara shiri da wuri, domin tsadar farashin canjin dala ya zama kalubalen da a ke fafutukar daukar matakai don tabbatar da rangwame da walwalar maniyyata.
Sakataren hukumar kuma mukaddashin shugaban kwamitocin biyu, Dakta Abdullahi Rabi’u Kontagora, ya ja hankalin wakilan kwamitocin da su yi aiki tsakani da Allah.
Ya ce: “Don tabbatar da duk kamfanin da a ka bai wa aikin yana da kayan aiki da muradin kare rayukan maniyyata.”
Daraktan kamfanin Max Air, Dikko Dahiru Mangal, ya ce a shirye su ke su tunkari kwamitin tantancewar.
“Muna da ingantattun kayan aiki don gudanar da wannan aiki.”
Malam Ahmad Bashir Bulma na kamfanin dakon kaya na hukumar jiragen Nijeriya da ke Legas, ya ce wannan ba shi ne karo farko da suke kula da jigilar kayan alhazai ba.
“Muna da dukkan takardun da a ke bukata don haka mu ke maraba da wannan tantancewa.”
Wannan ya dai biyo bayan matsayar da hukumomin Saudiyya da hukumar alhazan Nijeriya suka cimma, na amincewa da kara yawan kamfanonin jiragen yawo da za su shiga hidimar jigilar alhazai zuwa guda 40.