Hukumar jin dadin alhazai ta kasa, NAHCON ta bayyana cewa za’a kammala jigilar Alhazan bana (2024) zuwa kasar Saudiyya a ranar 10 ga watan Yuni ko kuma kafin ranar.
Mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta NAHCON, Fatima Saada Usara ce ta bayyana hakan, inda ta kara da cewa, an kaddamar da jigilar Maniyyatan Nijeriya ne na bana a jihar Kebbi ranar Laraba, sannan kuma jirage biyu za su tashi dauke da maniyyatan jihar Nasarawa da babban birnin tarayya (FCT) a filin jirgin sama na Abuja.
- Hajjin Bana: Saudiyya Ta Kaddamar Da Kundayen Wayar Da Kai Ga Mahajjata Cikin Harsuna 16 Har Da Hausa
- Hajjin Bana: Ranar 23 Ga Watan Mayu Za A Fara Jigilar Maniyyatan Jihar Kaduna – Hukuma
Ta kara da cewa, Jirage biyu za su ci gaba da tashi a kowace rana daga bisani kuma a kara ya zama biyar a kowacce rana.
Usara ta kara bayyana cewa, an kebe filayen jiragen sama 15 don gudanar da aikin Hajjin 2024 tare da mahajjata 65,047 daga bangaren gwamnati da masu zaman kansu.
“Jami’an diflomasiyya, ma’aikatan Hukumar aikin hajji tare da mataimakin shugaban kasa, Mai girma Kashim Shettima ne, suka halarci taron kaddamar da jirgin farko na mahajjatan bana (2024),” in ji ta.