ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hajjin 2025: Yadda Alhazan Nijeriya 7 Suka Rasa Rayukansu A Saudi Arabiya

by Sulaiman
6 months ago
Hajji

A ranar Lahadi ne aka kawo karshen aikin Hajjin 2025, inda Alhazai suka koma masaukansu da ke garin Minna.

Jifan Shaidan da aka yi a rana ta uku, na nuni da cewa; an kawo karshen aikin na Hajjin banan, sai dai wadanda suka jinkirta dawafinsu.

  • Darussan Hadisin Aikin Hajjin Manzon Allah S.A.W (2)
  • Cikin Shekaru 2, Tinubu Ya Karɓo Bashi Fiye da Shugabannin Nijeriya 3 – Obi

Aikin Hajjin, na daya daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar, amma daga cikin biyun da ba a wajabta wa wadanda ba su da iko ba, wanda kuma dukkanin musulmi na kwadayin yi ko da kuwa sau daya ne a rayuwarsa, ya ga ya samu damar ziyarar kasar da aka yankewa Musulunci cibiya.

ADVERTISEMENT

Duk da cewa, ba kowadane Musulmi ba ne ke bayar da labaru ko rahotannin abubuwan da ke faruwa da su a wannan kasa mai tsarki ba.

Amma a Nijeriya, an samu rahotannin cewa; mahajjata bakwai sun mutu a yayin wannan aiki nasu na Hajjin bana, sakamakon rashin lafiya.

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Duk da cewa, yanayin zafi ya yawaita a kasar ta Saudiyya, yayin gudanar da aikin Hajjin 2025, koda-yake; akasarin wadanda suka mutu daga Nijeriyar tsofaffi ne.

Rasuwar farko da aka sanar ta wani Alhaji ce daga Jihar Oyo, Alhaji Sulaimon Hamzat, wanda ya rasu a ranar 17 ga Mayun 2025 a kasar ta Saudiyya.

Na biye da shi kuma daga Jihar Abiya ne, mai suna Alhaji Saleh, Shugaban Kasuwar Shanu ta Lokpanta, wanda ya rasu a garin Makka a daren ranar Litinin 26 ga watan Mayun 2025.

Bayan haka kuma, sai wata Hajiya mai shekaru 75 daga Jattu Uzairue a Karamar Hukumar Etsako ta yamma da ke Jihar Edo, Adizatu Dazumi, wadda ta mutu a ranar Litinin 26 ga Mayun 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya.

An samu rahoton cewa, Dazumi ta kamu da rashin lafiya jim kadan bayan kammala dawafi, inda aka garzaya ta ita zuwa asibitin Sarki Fahad da ke Makka a ranar Lahadi, washegari kuma ta mutu.

Haka zalika, wata Hajiya daga Jihar Filato ta rasu a birnin Makka da ke Saudiyya, yayin gudanar da wannan aiki Hajjin 2025.

Marigayiyar, mai suna Hajiya Jamila Muhammad, ta rasu ne sakamakon cutar Siga da ke fama da shi a asibitin Sarki Abdul’aziz da ke birnin Makka.

Kwana daya kafin fara aikin Hajjin 2025, wani Alhaji daga Jihar Kano mai suna Shu’aibu Jibrin, ya rasu a garin Makka.

Haka nan kuma, wani Alhajin Nijeriya ya rasu a filin Arfa.

A cewar Shugaban Hukumar Alhazai ta Nijeriya, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, “Mun samu labari mara dadi cewa; mun rasa mahajjatanmu a yau Arfat, dayan kuma ya rasu kafin mu bar Makka,” in ji shi.

Ya kuma ce, mutuwar Alhazan daga Allah ne; inda ya kawar da rade-radin da ake yin a cewa, zafin rana ne ya haddasa su.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Next Post
Majalisar Tarayya Na Ƙoƙarin Zama Ƴar Amshin Shata – Saraki

Majalisar Tarayya Na Ƙoƙarin Zama Ƴar Amshin Shata - Saraki

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.