Hukumar Aikin Hajji da Umarah ta Kasar Saudiyya ta gabatar da wasu kundaye 15 da za su taimaka wajen yi wa alhazai jagoranci da wayar da kai a kan aikin Hajji daga ko ina a fadin duniya, a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana a kasa mai tsarki.
Wannan ci gaba na daga cikin tsare-tsaren da hukumar ta gabatar domin wayar da kan al’umma a yayin aikin hajjin bana na shekarar 1445 bayan hijira wanda ya yi daidai da 2024.
- Hajjin Bana: Shettima Zai Kaddamar Da Jirgin Farko Na Maniyyata 430 A Kebbi
- Matashi Ya Banka Wa Masallaci Wuta Yayin Da Ake Sallah A Kano
Hukumar ta sanar da hakan ne a shafukanta na kafofin sada zumunta da kuma shafinta na Intanet: https://guide.haj.gov.sa/
Kundayen za su taimaka wa alhazai wajen amsa tambayoyin da aka fi yi cikin harsuna 16 da suka hada da Larabci, Inglishi, Faransanci, Urdu, Bengali, Indonesian, Hausa, Amharix, Persian, Spanish, Turkish, Russina, Sinhalese, Uzbek da yaren Malaysia.
Kundayen za su taimaka wajen samar da bayanai da suka shafi kiwon lafiya, kwatance, harkar shari’a cikin tsarin taswira, kananan bidiyo da hotuna masu fadakarwa.
Bugu da kari akwai tsarin da aka ware inda alhazai za su saurari sautin murya don samun bayanai cikin sauki ta yadda za su fahimci abubuwan da suka shige musu duhu a kan aikin Hajji.