• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hajjin Bana: Jihohi 11 Sun Kashe Naira Biliyan 6.2 Kan Mahajjata

byYusuf Shuaibu
4 months ago
Hajji

Rahotanni sun bayyana cewa kowanni mahajjaci daga cikin su 3,345 ya samu Riyal 50 na Saudi a matsayin tallafi a lokacin bukukuwan Sallah da kuma saukaka musa lokacin zaman su a kasar mai tsarki.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin wakilin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda shi ne shugaban kwamitin wakilin na mahajjatan Jihar Kano, Sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Maharaz Karaye.

  • Duk Da Jihohin Nijeriya Sun Fara Biyan Mafi Ƙarancin Albashi Na 70,000, Ana Ci Gaba Da Fuskantar Matsin Rayuwa
  • Hadin Gwiwa Da Sin Na Bunkasa Zaman Lafiya Da Daidaito A Yankin Kahon Afirka

Sarkin ya isar da sakon gwamnan a yayin da yake yi wa mahajjatan Jihar Kano jawabi a gidan Shari Mansur a Makkah, sarkin ya isar da sakon Gwamna Yusuf.

Sakataren Kwamitin kuma Daraktan Janar na Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta a Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ya ce tsarin rarraba kudin ya gudana cikin cikakken tsari.

Ya kuma ce ya sanar da karin tanadi ga mahajjatan, wanda zai ga kowannensu ya karbi babban akwati na tafiya a shirin dawowarsu gida.

LABARAI MASU NASABA

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (1)

Babban Al’amari Ne A Samu Ƴar Shekara 6 Ta Haddace Qur’ani A Makarantar Raudatul Jannah – Mai Sikeli

Haka zalika, Gwamnatin Jihar Kebbi ba ta bayar da tallafi ga mahajjantanta 3,800 daga jihar ba. Amma a kasar Saudiyya, Gwamnan Nasir Idris ya amince da bayar da Riyal 200 ga kowane alhaji daga jihar.

Gwamnatin Jihar Lagos ba ta tallafi ga mahajjatanta a wannan shekara ba, yayin da kowane daga cikin masu aikin hajji 1,315 daga jihar ya biya kimanin naira miliyan 9.

Amma kuma, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ba kowane daga cikin mahajjatan kyauta Riyal 180, wanda ya kai naira 98,454,050 gaba dayansu.

Gwamnatin Jihar Jigawa, wacce ma ba ta bayar da tallafi ga mahajjatanta ba a wannan shekarar, amma ta ba su kyautar Riyal 100 (kimanin naira 43,000) ga kowanne daga cikin mahajjatanta 930.

Dukkanin alhazai Jihar Sakkwato 3,200 sun karbi Riyal 1,000 (wanda ya kai kimanin naira 450,000) a matsayin kyautar sallah daga Gwamna Ahmed Aliyu.

Gwamnan ya sanar da hakan a ranar Asabar yayin ziyararsa ga tawagar alhazan jihar a Mina da ke kasar Saudiyya, inda ya taya su murnar kammala aikin hajj cikin nasara.

Mataimakin gwamnan Jihar Borno, Umar Usman Kadafur, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta biya kudin hadiyya ga kowane alhazi daga jihar. Adadin alhazan sun kai 2,174, da suka yi aikin hajji a wannan shekara daga jihar.

Wani masani kan harkokin al’umma, Farfesa Yahaya Tanko, a cikin wata hirar, ya bayyana cewa kashe kudin da gwamnonin suka yi kan aikin hajji ba matsala ba ce, amma sun manta da asalin abin da al’ummarsu suka fi bukata.

Ya ce ya kamata gwamnonin su fi mai da hankali kan magance matsalar tsaro da inganta jin dadin ‘yan kasa.

Da yake jawabi kan lamarin, babban limanin Al-Habibiyah Islamic Society (AIS), Sheikh Fuad Adeyemi, ya ce ba laifi ba ne ga gwamnatin tarayya da na jihohi su tallafa wa masu alhazai, amma ya kamata a yi amfani da kudaden wajen abubuwan da mutane suka fi bukata.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (1)
Addini

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (1)

July 4, 2025
Babban Al’amari Ne A Samu Ƴar Shekara 6 Ta Haddace Qur’ani A Makarantar Raudatul Jannah – Mai Sikeli
Addini

Babban Al’amari Ne A Samu Ƴar Shekara 6 Ta Haddace Qur’ani A Makarantar Raudatul Jannah – Mai Sikeli

June 22, 2025
Za Mu Tabbatar Da Yin Aiki Da Ƙungiyar Mahaddata Alƙur’ani – Daurawa
Addini

Za Mu Tabbatar Da Yin Aiki Da Ƙungiyar Mahaddata Alƙur’ani – Daurawa

June 21, 2025
Next Post
Za Mu Tabbatar Da Yin Aiki Da Ƙungiyar Mahaddata Alƙur’ani – Daurawa

Za Mu Tabbatar Da Yin Aiki Da Ƙungiyar Mahaddata Alƙur'ani - Daurawa

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version