Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bukaci maniyyatan jihar zuwa Saudiyya su kasance masu biyayya da bin doka da oda, kuma su kasance jakadu na gari ga jihar da Nijeriya a yayin da suke ƙkasa mai tsarki.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya yayin jawabin sa na bankwana ga maniyyatan jihar a hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Gombe, “Yayin da kuke kasa mai tsarki, don Allah ku kasance jakadu nagari ga kanku, da al’ummarku, da kananan hukumominku, da Jihar Gombe dama Nijeriya, don mu yi alfahari da ku,” in ji shi.
Da yake kira ga maniyyatan su nesanta kansu daga duk wani abu da ka iya bata musu aikin na Hajji, ko taba mutuncin su ko na Jihar Gombe, Gwamna Inuwa ya tunatar da su cewa a kasa mai tsarki doka tana aiki ba sani ba sabo kan duk wadda aka kama da aikata laifi ko rashin gaskiya.
Da yake yi wa maniyyatan fatan gudanar da karbabben aikin Hajji, gwamnan ya karfafa su da su rika tambayar jagororinsu kan duk wani abu da ya shige mu su duhu. Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen ganin alhazan jihar sun yi aikin Hajji cikin natsuwa tun daga Nijeriya har zuwa kasa mai tsarki.
Da yake tsokaci kan matsalolin rayuwa dana tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar nan, Gwamna Inuwa Yahaya ya buƙaci maniyatan su zage damtse wajen yin addu’o’in Allah ya samar wa kasar mafita.
Gwamnan ya kuma bukaci jami’an hukumomin alhazai a dukkan matakai su gudanar da ayyukan su cikin gaskiya da amana da kishin kasa don gudanar da aikin Hajjin cikin nasara.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Gombe, Mai Martaba Sarkin Dukku, Haruna Abdulkadir Rasheed, ya yaba wa gwamnan bisa jajircewarsa na ganin an gudanar da aikin Hajji na bana cikin nasara.
Da yake jan hankalin alhazan jihar su maida hankali ga ibada maimakon sayen tsaraba, shugaban ya bukaci maniyyatan su ba da hadin kai ga jami’an aikin Hajji na jiha da na kasa don samun nasarar gudanar da aikin.
A jawabinsa na maraba, babban sakataren hukumar Alhaji Sa’adu Hassan, ya yaba wa gwamnan bisa samar da ingantaccen masauki ga maniyyatan jihar a ƙasa mai tsarki.
Ya ce da farko jirgi mai daukar alhazai 350 aka tsara zai yi jigilar alhazan jihar, amma bisa jajircewar da gwamnan ya yi, yanzu an samar da jirgi mai daukan mutum 550 da zai tashi da sawun farko na maniyyatan jihar. Ya ce bayan tantance maniyyatan da aka lika sunayensu, za a fara jigilar mahajjatan gadan-gadan a gobe Laraba.