Hukumar kula da jin dadin da alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta ware ranar 6 ga watan Mayu domin fara jigilar maniyyata daga nan gida Nijeriya zuwa kasa mai tsarki ga wadanda za su sauke farali a shekarar 2025.
Da yake magana a yayin sanya hannun yarjejeniya da zababbun kamfanonin jiragen da za su yi aikin jigilar maniyyata a ranar Litinin a Abuja, Kwamishinan ayyuka, bin sawu da lasisi na NAHCON, Prince Anofi Elegushi, ya ce, wannan na daga cikin shirye-shiryen da kamfanonin jiragen ke da shi domin jigilar maniyyatan Nijeriya.
- Wata Rana Za A Yi Wa Gwamnatin Tinubu Sambarka – Minista
- Hadin Gwiwa Karkashin BRI Mai Inganci Na Ingiza Ci Gaban Duniya
Idan za a iya tunawa dai hukumar NAHCON ta sanar da cewa kamfanonin jiragen Mad Air, Air Peace, UMZA Airline da FlyNas ne aka zaba domin jigilar adadin maniyyata 52,000 da aka amince wa Nijeriya.
Elegushi ya bukaci kamfanonin jiragen saman da su yi duk mai yiyuwa wajen tabbatar da sun yi aiki mai inganci domin samun gudanar da jigilar cikin nasara da kwanciyar hankali.
Ya ce a wannan shekarar za su ga an biya su kudin kwantiraginsu cikin gaggawa, amma hakan zai kasan biya kan naira a jigilar daga Nijeriya da kuma biya kan Riyal na Saudi a yayin kwasowa daga Saudiya.
“Muna kokarin kawar da bangaren dala. Abin da muke so mu yi shi ne mu biya a cikin kudin gida na duk kamfanonin jiragen sama. Kuma za a biya kudin ne daidai da farashin dala a halin yanzu a lokacin da ake biya.
“Kason da ya dace ya ba ku damar gudanar da ayyukanku dukkan ne za a biya ku, bayan kammala aikin za a karasa biyanku sauran,” ya shaida.
Tun da farko, shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman Saleh, ya ce, ayyukan jirage na sufuri na daga cikin muhimman ayyukan da ke gabansu wajen sauke nauyin aikin hajji.
“Lamarin na bukatar kwarewa matuka gaya da kuma himma da azama. Wannan lamarin ba kawai ga batun sufuri ba ne, ya shafi har da ciki alkawuran da aka dauka da mutuntaka da kariya hadi da saukaka wa maniyyata.”
Ya ce kamfanonin jiragen sama da aka yi aikin sun gudanar da cikakken tsarin zabe bisa cancanta, amintacce da kuma ingantaccen aiki.
“NAHCON ta yi taka-tsan-tsan wajen tabbatar da cewa kamfanonin jiragen sama masu inganci, ingantattun kayan aiki da fasinja ne kadai aka damka wa wannan gagarumin aiki.
“Kwarewarku da tarihinku na gudanar da manyan ayyuka, musamman ayyukan da suka shafi aikin hajji, sun ba mu kwarin gwiwa kan iyawar ku na gudanar da jigilar hajji cikin sauki.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp