Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun kai samame a otal din Emerald dake unguwar Ladipo a Oshodi a jihar Legas inda sukayi kichibis da wasu maniyyata suna tsaka da hadiye kulli-kulli na hodar iblis gabannin tashin jirgin su zuwa kasa mai tsarki domin gabatar da aikin hajji a ranar Laraba 5 ga Yuni 2024.
Wadanda aka kama yayin samamen sun hada da: Usman Kamorudeen mai shekaru 31; Olasunkanmi Owolabi, 46; Fatai Yekini, 38; da wata mace mai suna Ayinla Kemi mai shekaru 34. Mutanen hudu sun kama dakunan otel biyu ne, inda suka tanadi kullin hodar iblis 200 wanda nauyin sa ya kai Kilogiram 200 don hadiyewa.
- Samun Bunkasuwa Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
- Yadda Gwamnan Zamfara Ya Ƙaddamar Da Adaidaita Sahu 650 Da Babura 1000 A Sokoto
Da yake yabawa kwamanda, da jami’an hukumar NDLEA reshen jihar Legas, wadanda suka gudanar da aikin, shugaban hukumar, Burgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya ce hukumar za ta ci gaba da sa ido domin ganowa tare da kama miyagu wadanda za su so su fake a karkashin aikin hajji don aiwatar da munanan ayyukansu da ke iya zubar da kimar kasar.
Shugaban NDLEA ya kuma bayyana cewa “Hukumar za ta yi aiki tare da takwarorinmu na Saudiyya don ganin an gano wadanda suke jiran miyagun kwayoyin da aka kama din a kasar, tare da tabbatar da cewa sun fiskanci hukuncin da ya dace da su.