Hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON), ta bayyana cewa Nijeriya ba za ta yi amfani da sararin samaniyar kasar Sudan ba, wajen jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin bana.
Shugaban NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi ne, ya bayyana hakan a yau a wani shiri na gidan rediyon Freedom da ke Kaduna.
- Mutane 17 Sun Shiga Hannu Kan Hada-hadar Canjin Kudi Ba Bisa Ka’ida Ba A Kano
- Tinubu Ya Dawo Nijeriya Bayan Shafe Mako Guda A Turai
Malam Jalal Arabi ya tabbatar da Nijeriya ba za ta yi amfani da sararin samaniyar Sudan a lokacin tashin jiragen maniyyata saboda tsaro.
Don haka ya ce jiragen saman guda uku da aka bai wa kwangilar jigilar maniyyata da suka hada da MaxAir da Peace Air da kuma Flynas sun shirya tsaf domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Ya kuma bayyana cewa a ranar 15 ga watan Mayu ne, za a fara jigilar maniyyatan Nijeriya daga jihar Kebbi zuwa kasa mai tsarki a filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi.
Arabi, ya kuma bayyana cewa ana sa ran tawagar farko ta ma’aikatan NAHCON da suka hada da likitoci da ‘yan jarida za su tashi zuwa kasa mai tsarki nan da kwanaki masu zuwa domin shirya tarbar maniyyata.