Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani kan zargin da wasu jama’a ke yi cewa ta ki gurfanar da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Doguwa a gaban kotu.
‘Yan sanda sun kama Doguwa a karshen watan Fabrairu, inda suka kai shi kotun majistare bisa zarginsa da harbe wasu mutane Uku da raunata takwas a mazabarsa kwana daya bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a yayin ayyana sakamakon zaben a mazabarsa ta Doguwa/Tudun wada.
Kotun dai, ta ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan yari, kafin fara shari’a gadan-gadan.
Sai dai, wata babbar kotun tarayya a Kano ta bayar da belin Ado Doguwa a ranar 6 ga watan Maris.
Tun daga lokacin kuma ba a sake jin duriyar komawa don ci gaba da shari’ar ba.
Lamarin dai ya sa bangarori da dama sun fara zargin ko hukumomi a Kano, na kokarin danne maganar, har ta bi ruwa.
To amma a martanin da ta mayar a ranar Laraba, ma’aikatar shari’ar jihar Kano ta ce ba da gangan, ta ki kai shi kotu ba.
A cewarta, jinkirin da aka samu wajen ci gaba da shari’ar, wani al’amari ne, na kokarin bin tsari don tabbatar da adalci ga kowanne bangare.
Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan ya ce, tun lokacin da aka fara gabatar musu batun Alhassan Ado Doguwa, suka lura cewa akwai kura-kurai.
”Don kuwa akwai wasu batutuwa da ba a shigar da su cikin takardun da suka shafi zarge-zargen da ake yi wa dan siyasar ba,” in ji shi.
A cewar kwamishinan hakan zai iya kawo cikas a shari’ar, ko da an ci gaba da sauraren ta a kotu a yanzun.
BBC HausaÂ