Ɗaya daga cikin jarumai masu tasowa, kuma wanda ya shafe tsawon lokaci a Masana’antar Kannywood, Muhammad Mu’azu ya bayyana cewa, ba komai ne yake sa a samu daukaka a rayuwa ba, musamman a Masana’antar Kannywood; da ya wuce hakuri da biyayya ba.
Muhammad, wanda ya fara wannan harka ta shirin fim tun a shekarun kuruciya, yana daya daga cikin jaruman da Allah ya yi wa baiwar nishadantar da masu kallo a cikin fina-finansa.
- Fina-finai Masu Dogon Zango A Masana’antar Kannywood: Ci Gaba Ko Akasin Haka?
- Yawan Tikitin Kallon Fim Din “Ne Zha 2” Da Aka Sayar a Karshen Mako Ya Shiga Sahun Gaba Na Fina-Finai 5 A Arewacin Amurka
Mu’azu, wanda kani ne ga furudusa kuma jarumi Usman Mu’azu, na daga cikin jaruman da suke kayatar da masu sha’awar fina-finan Hausa.
Da yake amsa tambayoyi a wata hira da ya yi da Freedom Radiyo, jarumin ya yi karin haske dangane da maganganun mutane da ke yi na cewa, halin da ya nuna a cikin shiri mai dogon zango na Labarina, da ya fito a matsayin wani mutum mai son abin duniya, ko a zahiri ma haka yake? Muhammad ya ce, ko alama ba haka yake a zahiri ba, domin kuwa shi mutum ne wanda ba ya dora wa kansa son tara abin duniya.
“Ni ba irin mutanen nan da ke sha’awar tara abin duniya ba, ya kamata mutane su sani cewa, ba lallai halayyar da ka nuna a cikin shirin fim ya zama ko a zahiri haka kake ba, idan ina da abin da zan yi da kudi, to muddin na samu wannan adadi na kudin, bana wahalar da kaina wajen neman wasu da zan ajiye a asusu, Umar na Labarina daban, haka zalika Muhammad Mu’azu daban”, in ji shi.
Daga karshe, jarumin wanda ya shafe shekaru fiye da 10 a Masana’antar Kannywood, ya shawarci matasa masu sha’awar shiga harkar fim, su tabbatar sun zama masu hakuri da biyayya ga na gaba da su, muddin suna son samun nasara a rayuwarsu ta jarumai.
“Dole ne ka kasance mai hakuri a rayuwa, domin kuwa babu wanda ya zama wani abu ba tare da ya sanya hakuri a cikin al’amuransa na yau da kullum ba, duk wanda ka gani ya zama wani abu, ko ya samu wata daukaka ko shahara a rayuwa, to dole akwai kalubalen da ya fuskanta, domin kuwa ko a makaranta sai an ware wani lokaci da za a yi jarrabawa; domin gane masu fahimta da wadanda ba sa fahimta”.
Haka zalika, dole ne ka kasance mai biyayya a duk inda ka samu kanka, muddin kana so kai ma wata rana a yi maka biyayya, musamman a masana’anta irin ta Kannywood, duk manyan jarumai irin su Ali Nuhu, Hadiza Gabon da sauran makamatansu; sai da suka yi biyayya, suka kuma yi hakuri kafin su kai matsayin da suke kai yanzu, in ji Muhammad.