Daya daga cikin mamallakan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Sir Jim Ratcliffe ya bayyana cewa, dole magoya bayan kungiyar su yi hakuri da tsare-tsarensa bayan kasancewarsa guda cikin mafiya rinjayen hannun jari a kungiyar.
Cikin watan Fabarairu ne Ratcliffe ya kulla yarjejeniyar sayen kashi 27.7 na hannun jarin Man-chester United kan yuro biliyan 1 da miliyan 250 kuma tun daga wancan lokaci ya ke gabatar da gyare-gyaren da ya ce su ne za su daga darajar kungiyar domin dawo da kimarta.
- Zargin Badakala: Tataburzar EFCC Da Yahaya Bello Na Daukar Sabon Salo
- Hajjin Bana: NAHCON Ta Ba Jihohi Wa’adin Mika Sunaye Maniyyata
A cewar Ratcliffe mai shekaru 71 tafiya ta fara nisa a gyare-gyaren da ya ke a United, kungiyar da yanzu haka ke matsayin ta 7 a teburin firimiyar Ingila ko da ya ke ta samu tikitin wasan karshe na cin kofin FA bayan doke Cobentry da kyar.
Sai dai amma duk da wannan nasara ta United akwai jan aiki a gabanta, lura da yadda ta ke shirin haduwa da takwararta Manchester City a wasan karshe na gasar ta cin kofin FA, kuma ma-su sharhi na ganin abu ne mai matukar wuya tawagar ta Manchester United ta iya kai labari a hannun yaran na Pep Guardiola wadanda damar lashe kofin zakarun Turai ta kufce musu bayan shan kaye a hannun Real Madrid ta Spain.
Ratcliffe ya ce sabbin gyare-gyare na tafe zuwa karshen kakar wasa kuma dole sai magoya baya sun yi hakuri, batun da ke kara tabbatar da jita-jitar yiwuwar kungiyar yin canje-canjen ‘yan wasa ciki har da mai horarwa Erik ten Hag, wanda ake ta rade radin cewa kungiyar za ta kora.