…Ci gaba daga makon jiya
6) Yayin da shirun ya zama amsa
Hausawa na da wani zancen hikima da ke cewa, “shiru ma amsa ne”. Akwai lokuta da dama da shiru yake zama babbar amsa a kan wata tambaya ko furta wasu kalamai ga abokan magana. Yin shiru a maimakon magana kan wasu al’amura kan isar da kyakkyawan sako cikin hikima. Yi tunani mana. Ka taba tambayar kanka game da karfin da ba da amsa ta hanyar shiru yake da shi? Ko ka taba tsintar kanka a wani yanayi da furta magana ba za ta gamsar da abokin magana ba ko da kuwa za ka dauki lokaci mai tsawo kana magana? Na san ka taba ji ana ce wa wasu mutane “ku rabu da wannan mai gardaman, ko za ku kwana kuna masa magana ba zai gamsu ba ko ba zai fahimce ku ba.” To a irin wannan yanayi, shiru shi ne babbar amsa da zai wadatar. Don haka kar a manta, yin shiru ba yana nufin ba ka da amsar da za ka bayar ba ne, a’a, shirun shi ne amsa.
7) Lokacin da ka san ko ka yi magana ba za a ji ba
Yana da kyau idan za ka yi magana, ka tsaya ka yi tunani, shin abin da za ka fada gaskiya ne, sannan wajibi ne ka fade shi, wane tasiri abin zai yi, za ka gyara ne ko za ka bata?
Duk iya kalamanka, akwai wani yanayi na rayuwa da za ka tsinci kanka a ciki wanda ko ka yi magana ba zai sauya komai ba. Watakila kana zance ne da wani aboki mai matukar gardama kamar dan jaki ko tafka muhawara mara ma’ana da ba za ta amfanar ba ko kuma wani yanayi da aka riga aka yanke hukunci a kai wanda ba zai yiwu a canza ba. A irin wannan yanayi, furta magana za ta iya kara rura wutar rikici ko tayar da zaune tsaye, don haka yin shiru a irin wannan yanayi shi ne mafita. Kamewar da ka yi a nan, ba yana nufin ka amince da wani abu da ya kamata a gyara ba ne, a’a, sai don kauce wa tayar da jijiyoyin wuya da babu gaira babu dalili, sai in abin zai iya kaiwa ga rasa rai, to sai a yi magana cikin hikima. Shi ma idan ka fada aka ce ba a amince ba, to sai ka shafa wa kanka lafiya, ka san cewa ba ka da iko a kan komai na jama’a.
8) Lokacin da kake magana
Dan jira, me ka ce? Yin shiru lokacin da kake magana kuma? Na san watakila mai karatu ya ji abin bambarakwai ko? To bari mu ji yadda abin yake.
A lokuta da dama, za ka iya jin wani yana cewa “da gangar na yi kaza da kaza”, wannan yana nufin akwai abin da za ka iya yi don kawata maganar da kake yi domin isar da wani muhimmin sako. Ba zan manta ba, a lokacin bikin aurena, malamin da yake mana jawabi, ya rika yi yana dan yi shiru na takaitaccen lokaci a daidai lokacin da mutane ke tsammanin zai ci gaba da maka ba tsayawa. Misali, ya fadi sunan ango, sai ba I ce amarya ba nan da nan sai da ya yi dan shiru tukuna, sai da dukkan hankula suka kara tattaruwa suka koma kansa sannan ya fadi amarya. Wannan sai ya kara wa nasihar da yake yi amrmashi.
Haka nan na taba halartar bikin karrama wasu da suka shiga gasa, da mai sanar da wadanda suka zamo zakara ya zo wurin da zai fadi sunayensu, sai ya rika yin shiru na takaitaccen lokaci. Misali, wacce ta zo ta uku a wannan gasa ita ce…. (sai ya yi shiru), mutanen da ke wurin kuma kowa hankalinsa ya koma kan mai gabatarwar.
Haka nan ana bukatar ka yi shiru ka yi tunani kafin ka bayar da amsa idan wani abu na gaggawa ya afko ma. Wannan zai taimaka wajen yin tunani mai kyau da zabar amsa mafi dacewa da za ka bayar.
Yin shiru ba alama ce ta tsoro ba, a lokuta da dama, shiru na zama wani babban makami na gyara kanka ko tarwatsa kanka. Don haka, amfani da shiru a lokutan da suka fi dacewa da hakan wani sinadari ne na kyautata jin dadin rayuwa.