Marubuciyar yanar gizo, da ita ma take kan ganiyarta AMINA MA’AJI ta yi ikirarin cewa ko daya ba sa wa maza wani zambo ko habaici a cikin rubuce-rubucensu face gaskiyar halayen mazan da suke fada a inda ta kama. Ga dai tattaunawarsu da ADAMU YUSUF INDABO kamar haka:
Wace ce Amina Ma’aji?
Assalamu Alaikum. Cikakken sunana ke nan Amina maaji, wanda aka fi sani da Maman Khairat. Ni y’ar jahar Yobe ne a Potiskuma, nan aka haife ni na yi rayuwa, nan na yi karatu tun daga kan primary har i zuwa makarantan hurar da malamai ‘Federal College Of Education (Technical) Potiskum’ inda na karanci mathematics and computer, na gama a shekarar 2015. Yanzu haka kuma ina aure ne a garin Damaturu. Ina da yara guda hudu maza biyu mata biyu.
A duniyar rubutu mun san wata marubuciya Ummi Ma’aji, sai kuma ga Amina Ma’aji ta bayyana. To mene alakarki da ita?
Sunane kawai ya zo daya, amma Ummi Ma’aji bana da alaka ta jini da ita face ta musulunci, sai ta rubutu, kuma daya daga cikin gwanayen marubutana, so na dade da sanin ta, kuma ina bukatan haduwa da ita. Amma har yanzu Allah bai kaddara haduwarmu ba.
To mene tarihin kasantuwar ki a cikin duniyar rubutu?
Tun farko ni mai son karance-karance ne, tun ina Jss 2 nake son karatu nakan dauki takaddata in ta rubuta labari sosai, da na je ss 1 ni ce mai karanta littafi a mutane da labari mai dadi. Yayin da na gama makaranta, sai karatun ya shiga raina, mahaifiya ta takan ba ni kudi in siyo littafi dan in karanta. Na fara karanta littafin Hadiza Salisu shareef ‘SO’ ya yi mun dadi sosai na samu darasi a cikin littafin, darusa kuma masu yawan gaske. Allah Ya ji kan ta Amin. Daga sai na zama mai karance-karance da yawa. Akwai wata marubuciya Sa’adatu Wazeeri Gombe ita ce ta fara ba ni shawara in yi rubutu dan ta ga ina da fahimtar abu da wuri. Na ce mata babu kudi. To shi ne na tambayi wani ana ce mishi Adamu dan tare muke karatu, yace in fara na tambayi kanina Musaddam shi ya fara ba ni goyon baya na rubuta littafina na farko ‘Namiji Karin Kunama’ na sha wahala wajen rubutawa saboda rashin sabo labarin cikin littafin, labarina ne na kaina. Amma a halin yanzu rubutu ya zame mini abunda ke sa ni farin ciki.
Ke nan Namiji Karin Kunama ne littafi na farko da kika rubutawa?
Kwarai, Shi ne littafina na farko a duniyan rubutu. Na rubutu ahi a karshen shekaran 2015. Daga shi ban sake littafi ba sai 2016.
Sunan littafin Namiji Karin Kunama, ya tabbatar da zargin da ake cewa littafan Marubuta mata, yawancinsu zambo ne da habaici wa maza. Wai me yake kawo haka?
To gaskiya ni dai bana rubuta littafin da bai faru da gaske, ba wasu hakan ne za su hanga a mahangarsu. Amma ni ai tarihin rayuwata ne na bayar a cikin littafin ‘Namiji Karin Kunama’ lokacin da na fada SO mai wuyar fassara, su mazan sun yi abun rubutun ne yawanci in ka ga mace ta yi rubutu a kan maza, daman can halinsu ne babu sharri. Allah ya sa mu dace. Kuma mu ma matan In labarin ya juyo gare mu mukan iya rubutawa. Kuma littafin ya yi duba ne ga maza masu janyewa daga masu yi musu halacci, ya yi duba a kan zurfafa soyayya daga karshe su wufce subar mutum da hamma, a kwai yaudara da cin mutunci ha’i ci, aikin da na sani.
Ya yi duba ne ga samari da ba su da komai mace takan zama da su a haka daga baya, in wadata ya zo musu ka neme su ka rasa su, kun sha wahala tare kudi ba tare da ku za a ci ba. To ka ga wannan duk halin maza ne, sai illa nadiran.
Za mu ci gaba makon gobe