Gamayyar matasa karkashin inuwar kungiyoyin matasa daga kowane sashi na kasar nan ta bayyana cewa barazanar da Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi, ta soke bayar da biza ga ‘yan Nijeriya munakisa ce da aka shirya domin a bata sunan gwamnatin tarayyar Nijeriya da kuma Babban Bankin Nijeriya (CBN).
Mambobin kungiyar tuntuba ta matasan Arewa da kungiyar matasa ta Ohanaeze Ndigbo da kungiyar matasan ta Oduduwa da matasan yankin Iyamurai, sun yi tir da wannan barazana ta soke bayar da izinin shiga kasashen na Daular Larabawan, da aka yi.
- Xi Ya Bukaci A Yi Kokari Cikin Hadin Kai Wajen Cimma Burikan Babban Taron Wakilan JKS
- Barazanar Kai Hari Abuja: Buhari Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Kwantar Da Hankalinsu
A wata sanarwa da gamayyar wadannan kungiyoyin ta bayar ta hannun babban sakatare, Ohanaeze da kuma Nwada Chiama, ta ce, barazanar da kungiyar hadaddiyar daular Larabawan ke yi na da nasaba da bin sawun kudin da ake kashewa daga Nijeriya zuwa kasashen.
Gamayyar ta ce in za a iya tunawa ma fi yawan jiragen da ake zirga-zirga zuwa saular mallakar gwamnatin daular Larabawan ne.
Saboda haka suka ce,“Muna fada da babbar murya cewa wannan matakin an dauke shi ne, domin dakile wasu harkoki a wannan kasa tamu. In za a iya tuna wa Babban bankin Nijeriya ya fitar da dala miliyan 110 domin canjin kudaden kasashen waje kan harkar sufurin jiragen sama a cikin watan Agusta sannan kuma ta sake fitar da dala miliyan 120 a ranar 31, ga watan na Okotoba.