• English
  • Business News
Tuesday, June 24, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hannu Daya Ba Ya Daukar Jinka——Sin Da Afirka Za Su Kara Cimma Nasarorin Yaki Da Kwararar Hamada In Sun Hada Kansu

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Hannu Daya Ba Ya Daukar Jinka——Sin Da Afirka Za Su Kara Cimma Nasarorin Yaki Da Kwararar Hamada In Sun Hada Kansu
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Watan Yuni da muke ciki wata ne da ke shafar kiyaye muhalli, kasancewar ana samun ranar kare muhallin duniya da ma ranar yaki da kwararowar hamada da fari ta duniya, duk a wannan wata, wadanda suke jan hankalinmu game da muhimmancin zaman jituwar ‘yan Adam da muhallinsu. 

A nan kasar Sin, manufar samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba na kara zame wa ‘yan kasar jini da tsoka a rayuwarsu ta yau da kullum. Tun daga shekarar 2012, kasar Sin ta fara gudanar da wani babban aikin dasa bishiyoyi a fadin kasar, kuma kawo yanzu fadin dazuzzukan da aka dasa a wannan aiki ya kai eka miliyan 68, matakin da ya sa kason dazuzzukan a fadin kasar ya karu zuwa kashi 24.2%, kuma fadin dazuzzukan da aka dasa ma ya zo na farko a duniya, an kuma cimma gagaruman nasarori a fannin yaki da kwararowar hamada.

  • Firaministan Kasar Sin Ya Jaddada Hadin Kai Da Hadin Gwiwa A Taron Davos

Musamman ma dazuzzukan da aka dasa a sassan arewaci da arewa maso yammaci da ma arewa maso gabashin kasar, wadanda ake yi musu kirarin “babbar ganuwa mai launin kore”, sun taka muhimmiyar rawa ta fannonin kiyaye muhalli da bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma.

Nasarorin da aka cimma ta fannin inganta muhallin zama ba alkaluma ba ne ga al’ummar wannan kasa, kyautatuwar muhallin zama ne da suke gani da ido. Misali a birnin Beijing da nake rayuwa, a cikin ‘yan shekarun baya, dazuzzukan da aka dasa musamman domin mazauna birnin su shakata ko motsa jiki sun yi ta karuwa, kuma iska ma na kara inganta…kuma duk wadannan sauye-sauyen da ke faruwa ga rayuwata suna faranta mini rai sosai, amma abin da ya fi sa ni farin ciki shi ne yadda kasar Sin ke kokarin raba ingantattun fasahohinta ta fannin kyautata muhalli ga aminanta na Afirka, kasancewar a kwanakin nan na samu damar halartar kwas din samar da fasahohi wajen shuka shingen itatuwa mai suna Pan-African Great Green Wall (PAGGW), wanda aka shirya a jihar Xinjiang ta kasar Sin, inda na gane ma idona yadda masana da suka zo daga kasashen da ke kudu da hamadar Sahara, ciki har da na Nijeriya da Nijer da Mauritania da Habasha da sauransu suka hadu da takwarorinsu na kasar Sin, don su gano bakin zaren warware matsalar kwararowar hamada.

Kwararowar hamada babbar matsalar muhalli ce da ke barazana ga rayuwar dan Adam da ma bunkasuwarsu, kuma da kasar Sin da nahiyar Afirka dukkansu na daga cikin yankunan duniya da matsalar ta fi addaba. Taklimakan, hamada ce mafi girma a kasar Sin, wadda take jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin, kuma ma’anar Taklimakan shi ne “in ka shiga, ba lallai ne ka fita ba”, a sakamakon irin mummunan yanayin da ke wajen. To, sai dai duk da irin wannan hali, an gina wata hanya mai tsawon kilomita sama da 520 da ta ratsa hamadar, kuma domin kare hanyar daga kwararowar hamada, kana a gefunan hanyar, an dasa dazuzzuka masu fadin sama da mita 70, wadanda tsayinsu ya kai kilomita sama da 430.

Labarai Masu Nasaba

Sabuwar Shugabar Kwamitin Wasannin Olympics Na Duniya Na Fatan Sake Ziyartar Kasar Sin

Xi Jinping Zai Halarci Bikin Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan Da Yakin Kin Tafarkin Murdiya

Mista Innocent Alenyi da ya halarci kwas din, wanda shi ne mataimakin darektan hukumar kula da aikin PAGGW a tarayyar Nijeriya, bayan da ya kai ziyara wannan hanyar da ta ratsa hamadar Taklimakan tare da gane ma idonsa dazuzzukan da aka dasa a gafunan hanyar, ya fada min cewa, “Abin da ya fi burge ni shi ne yadda suke samar da ruwa ga wadannan bishiyoyin, inda na ga sun haka rijiyoyi fiye da dari a dab da hanyoyin mota, don samar da ruwa ga dashen tsare rairayi. Wannan hanya, tsawonta ya kai fiye da kilomita 500, kana dimbin bishoyoyin da aka dasa don kare hanyar tsawonsu ma ya wuce kilomita 430. Gaskiya abun da na gani ya ba ni mamaki. Kuma muna son yin amfani da wadannan fasahohi wajen dakile kwararar hamada a Najeriya.”

“Da rogo aka yi wannan gidan dara ko Checkerboard da Turanci na kare kwararowar hamada, kuma gwajin da ake yi yanzu ya shaida cewa, yana iya jure tsananin zafi da kuma sanyi, kuma tsawon shekarun yin amfani da shi zai iya zarce shekaru 10”. Umar Danladi Dahiru, wanda shi ne darektan cibiyar dake rajin kare kwararowar hamada a kasashen Afirka (Africa Desertification Control Initiative Nigeria), shi ma yana daga cikin masu halartar kwas din, a yayin da yake ziyara a hamadar Taklimakan, wani gwajin da ake yi ya ba shi sha’awa matuka, kuma ya ce, in dai an cimma nasarar gwajin, yana fatan za a yayata wannan sabuwar kayan kare kwararowar hamada zuwa kasashen Afirka.

Yanzu fasahohin zamani na kara taka muhimmiyar rawa a fannin dakile yaduwar hamada. A kasar Sin, an kafa cibiyar nazarin bayanan da aka tattara ta yanar gizo ta Internet don taimakawa samun ci gaba mai dorewa a shekarar 2021. Wannan cibiya ita ma tana samar da taimako ga kasashen Afirka. Li Xiaosong, wani mai nazarin kimiyya da fasaha ne dake aiki a cibiyar, shi ma ya bayyana yadda kasar Sin ke aiwatar da hadin gwiwa da kungiyar PAGGW, don yin amfani da fasahohin zamani ta fannin kyautata ingancin aikin yaki da kwararowar hamada, ya ce, “Aikinmu shi ne sa ido kan sakamakon da aka samu. Misali, a baya ba mu san ainihin sakamakon wasu ayyukan da muke yi ba, kuma ba a san ko ya kamata a ci gaba da gudanar da su ba. Saboda haka, yanzu muna yin amfani da taurarin dan Adam wajen gudanar da ayyukan sa ido a kai a kai, don duba ko matakan da aka dauka sun dace, kuma ko ana bukatar gyara dabarun.”

A tsawon kwanaki sama da 10 da ake gudanar da wannan kwas, irin musayar ra’ayoyi da fasahohi a tsakanin sassan biyu ba sa lissaftuwa. Burin bai daya na kyautata muhallin zama ya kusantar da kasar Sin da kasashen Afirka da juna da ma karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu.

Hannu daya ba ya daukar jinka, Marcelin Sanou, wani babban jami’i a sakatariyar kungiyar PAGGW, da wannan jimla ne ya bayyana hadin gwiwar Sin da Afirka ta fannin yaki da kwararowar hamada. Shi ma mista Endrias Geta Beldeda, mataimakin ministan kula da ban ruwa da shimfidaddun yankuna mara tudu na kasar Habasha, yana ganin cewa, ta fannin yaki da kwararowar hamada, shawarar shuka shingen itatuwa mai suna Pan-African Great Green Wall na daga cikin muhimman fannoni da sassan biyu ke iya yin kokari tare. Kasancewar kasashen Afirka da kasar Sin suna da kyakkyawar hulda ta fannonin diplomasiyya da tattalin arziki da al’adu, wadda ake iya yin amfani da ita wajen tabbatar da kyakkyawar makomar bai daya gare su.

Kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, kuma Afirka nahiya ce da aka fi samun kasashe masu tasowa, kullum makomarsu daya ce. Ta fannin yaki da kwararowar hamada, tabbas za su kara cimma gaggaruman nasarori in sun hada gwiwa da juna.(Lubabatu Lei)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Jarumar Nollywood, Mercy Ta Sauke Farali A Saudiyya Bayan Ta Musulunta

Next Post

Manjo Janar Ochai Ya Zama Sabon Kwamandan NDA Na 32

Related

Sabuwar Shugabar Kwamitin Wasannin Olympics Na Duniya Na Fatan Sake Ziyartar Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Sabuwar Shugabar Kwamitin Wasannin Olympics Na Duniya Na Fatan Sake Ziyartar Kasar Sin

3 hours ago
Xi Jinping Zai Halarci Bikin Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan Da Yakin Kin Tafarkin Murdiya
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Zai Halarci Bikin Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan Da Yakin Kin Tafarkin Murdiya

4 hours ago
Shugaban CMG Ya Zanta Da Manyan Jami’an IOC
Daga Birnin Sin

Shugaban CMG Ya Zanta Da Manyan Jami’an IOC

4 hours ago
Likitocin Kasar Sin Sun Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Kyauta Ga Yara A Botswana
Daga Birnin Sin

Likitocin Kasar Sin Sun Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Kyauta Ga Yara A Botswana

15 hours ago
Tawagar Likitocin Kasar Sin Sun Duba Marayu Marasa Lafiya Fiye Da 200 Kyauta A Zanzibar Ta Tanzaniya
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Kasar Sin Sun Duba Marayu Marasa Lafiya Fiye Da 200 Kyauta A Zanzibar Ta Tanzaniya

16 hours ago
Za A Gudanar Da Taron Dandalin Davos Na Lokacin Zafi Karo Na 16 a Birnin Tianjin Na Sin
Daga Birnin Sin

Za A Gudanar Da Taron Dandalin Davos Na Lokacin Zafi Karo Na 16 a Birnin Tianjin Na Sin

17 hours ago
Next Post
Manjo Janar Ochai Ya Zama Sabon Kwamandan NDA Na 32

Manjo Janar Ochai Ya Zama Sabon Kwamandan NDA Na 32

LABARAI MASU NASABA

Sabuwar Shugabar Kwamitin Wasannin Olympics Na Duniya Na Fatan Sake Ziyartar Kasar Sin

Sabuwar Shugabar Kwamitin Wasannin Olympics Na Duniya Na Fatan Sake Ziyartar Kasar Sin

June 24, 2025
Xi Jinping Zai Halarci Bikin Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan Da Yakin Kin Tafarkin Murdiya

Xi Jinping Zai Halarci Bikin Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan Da Yakin Kin Tafarkin Murdiya

June 24, 2025
Shugaban CMG Ya Zanta Da Manyan Jami’an IOC

Shugaban CMG Ya Zanta Da Manyan Jami’an IOC

June 24, 2025
An Cafke Mutum 22 Kan Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato – Uba Sani

An Cafke Mutum 22 Kan Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato – Uba Sani

June 24, 2025
Manchester United Za Ta Biya Fam Miliyan 60 Don Ɗaukar Mbeumo Daga Brentford

Manchester United Za Ta Biya Fam Miliyan 60 Don Ɗaukar Mbeumo Daga Brentford

June 24, 2025
Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Mako 3

Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Mako 3

June 24, 2025
Iran Da Isra’ila Sun Amince Su Tsagaita Wuta – Trump

Iran Da Isra’ila Sun Amince Su Tsagaita Wuta – Trump

June 24, 2025
Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi

Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi

June 23, 2025
EFCC Ta Kama Tsohon Babban Jami’in NNPC Kan Zargin Satar Dala Biliyan 7.2

EFCC Ta Kama Tsohon Babban Jami’in NNPC Kan Zargin Satar Dala Biliyan 7.2

June 23, 2025
Likitocin Kasar Sin Sun Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Kyauta Ga Yara A Botswana

Likitocin Kasar Sin Sun Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Kyauta Ga Yara A Botswana

June 23, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.